Shugabancin kasa a 2023: Ni ne muryar matasa da mata, Gwamna Yahaya Bello

Shugabancin kasa a 2023: Ni ne muryar matasa da mata, Gwamna Yahaya Bello

  • Ana jajiberin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC, Gwamna Yahaya Bello ya ce shi ne muryar matasa, mata, nakasassu da dukkan 'yan Najeriya
  • Gwamnan ya ce in har ya samu takara a APC, babu shakka zai fara murnar cin zabe da karfe 2 na ranar zaben shugaban kasa a 2023
  • Ya sanar da cewa, da kwarewarsa tare da gogewar da ya samu a jihar Kogi, cikin wata 12 zai magance rashin tsaron Najeriya

Kafin zuwan zaben 2023, 'dan takarar shugabancin kasa kuma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Lahadi ya ce shi ne muryar matasan kasar nan.

Gwamnan ya bayyana hakan a shirin Siyasa na gidan talabijin na Channels, sa'o'i kadan kafin a fara zaben fitar da 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwani: Matasan Kano Sun Balle Zanga-Zanga kan Hukuncin Gwamnonin APC

Shugabancin kasa a 2023: Ni ne muryar matasa da mata, Gwamna Yahaya Bello
Shugabancin kasa a 2023: Ni ne muryar matasa da mata, Gwamna Yahaya Bello. Hoto daga Yahaya Bello Support Group
Asali: Facebook

"A watan Yunin shekarar nan zan cika 47. Har yanzu ina da kuruciya, ni ne muryar matasan kasar nan, muryar mata, muryar nakasassu kuma muryar 'yan Najeriya ba tare da dubi da addini, yanki ko kabila ba saboda mun kwatanta hakan a jihar Kogi," gwamnan yace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan APC ta ba shi dama ya zama 'dan takarar ta a zaben da za a yi shekara mai zuwa, gwamnan Kogin ya bugi kirji ya ce zai lallasa 'dan takarar PDP, Atiku Abubakar.

Ya yi ikirarin cewa zai fara murnar nasararsa tun karfe 2 na yammacin ranar zaben shugaban kasa idan ya samu tikitin takarar.

Bello, wanda ya yi bayani kan shirye-shiryensa na daidaita kalubalen tsaron Najeriya, ya tunatar da cewa lokacin da ya hau mulkin jihar Kogi a ranar 27 ga watan Janairun 2016, jihar na fuskantar kalubalen tsaro.

Kara karanta wannan

Manyan matsaloli 4 da ke gaban APC yayin da zaben fidda gwani ya gabato

A yayin da aka tambaye shi wacce hanya gare shi ta shawo kan matsalar tsaron, gwamnan bai bayar da amsa kai tsaye ba.

A maimakon hakan, ya yi bayanin cewa ya gwada kwarewarsa wurin shawo kan matsalar tsaro kamar yadda ya yi a jihar Kogi.

"Na gwada wannan da kyau a jihar Kogi. Da Izinin Ubangiji , za mu yi nasarar shawo kan matsalar cikin watanni 12 na mulkin Yahaya Bello a matsayin shugaban kasa," ya kara da cewa.

Zaben Fidda Gwani: Matasan Kano Sun Balle Zanga-Zanga kan Hukuncin Gwamnonin APC

A wani labari na daban, wata kungiyar da ake wa lakabi da matasan da suka damu da lamurran APC sun shirya zanga-zangar lumana a Kano inda suke kalubalantar shawarar da gwamnoni sha daya na jam'iyya mai mulki ta APC da suka yanke na mika mulki ga kudancin Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Yayin zantawa da manema labarai a wajen zanga-zangar a ranar Lahadi, shugaban kungiyar, Nura Bebeji ya ce yanke shawarar da gwamnonin suka yi sun yi hakan ne da gangan don kange shugabannin arewa masu jini a jika irin su Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi, daga takarar shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Bayyana Yankin Da Magajinsa Zai Fito a 2023

Ya bayyana cewa duk wani yunkurin da gwamnonin suka yi don hana wa 'yan Najeriya damar zabar ra'ayinsu ba zai haifar da 'da mai ido ba a zaben shekarar 2023 da ke karatowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng