2023: Kan Gwamnoni 10 a Arewa ya hadu, an samu Mutum na farko da ya janye takara a APC
- Gwamnan jihar Jigawa ya zama na farko da ya fita daga masu neman takarar shugaban kasa a APC
- Sauran Gwamnonin na APC ne suka bada sanarwar cewa Muhammad Badaru Abubakar ya janye
- Mai girma Muhammad Badaru Abubakar ya dauki wannan matsaya domin a ba ‘Yan kudu dama
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya fita daga cikin masu neman kujerar takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Kamar yadda Leadership ta fitar da rahoto, Muhammad Badaru Abubakar ne mutum na farko da aka ji ya janye takara a cikin masu neman shugaban kasa.
Gwamnan kuma mai neman yin takara a APC ya dauki wannan mataki ne bayan gwamnonin Arewa 10 sun hadu a kan a kai takara zuwa Kudu a 2023.
Gwamnoni 10 da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya suka ba Mai girma Muhammadu Buhari shawarar ya nemo magajinsa ne daga kudancin kasar.
A ranar Asabar, 4 ga watan Yuni, 2022, 3adannan gwamnoni na APC sun tabbatar da cewa Alhaji Badaru Abubakar ba zai shiga neman tikitin takaran 2023 ba.
Kamar yadda aka ji, wadanda suka cin ma wannan matsaya su ne: Aminu Bello Masari (Katsina), Abubakar Sani Bello (Neja), da Abdullahi A. Sule (Nasarawa).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Farfesa Babagana Umara Zulum (Borno), Nasir Ahmad El-Rufai (Kaduna), da Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe) da tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamakko.
Bello M. Matawalle (Zamfara), Simon Bako Lalong (Filato), Abdullahi Umar Ganduje (Kano) da shugaban gwamnonin APC, Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi).
The Nation ta ce a takardar da wadannan shugabanni suka aikawa Buhari da sa hannunsu, sun sanar da shi su na farin ciki da abokin aikin na su ya hakura.
“Mu na murna da matakin da abokin aikinmu, Mai girma Abubakar Badaru ya dauka na nuna kishin kasa wajen janye neman takarar shugaban kasarsa.”
- Gwamnonin
A baya an yi ta yada jita-jita cewa irinsu Kayode Fayemi ko David Umahi sun janye takarar, amma an tabbatar da cewa har zuwa yanzu, babu gaskiya a labarin.
Babu mamaki zuwa yau, a ji wasu su na ta janye takara bayan sun biya N100 ma sayen fam.
Osinbajo zai kai labari?
A baya mun kawo rahoto cewa akwai yiwuwar Gwamnoni za su goyi bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya zama ‘dan takararsu a APC a zaben shekarar badi.
A karshen makon nan aka fahimci Gwamnonin Kano, Ogun, Ekiti, Gombe, Nasarawa da Ebonyi sintiri su na ta sintiri a Aso Rock Villa a kan maganar takarar.
Asali: Legit.ng