Watakila magana ta canza, Gwamnonin APC su na ta haduwa da Osinbajo a Aso Villa

Watakila magana ta canza, Gwamnonin APC su na ta haduwa da Osinbajo a Aso Villa

  • Akwai yiwuwar Gwamnoni za su goyi bayan Farfesa Yemi Osinbajo ya zama ‘dan takararsu a APC
  • Gwamnonin Kano, Ogun, Ekiti, Gombe, Nasarawa da Ebonyi sintiri su na ta sintiri a Aso Rock Villa
  • Shi kuwa Bashir El-Rufai yace ya san wanda Muhammadu Buhari yake so a ransa, amma ya yi gum

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rahotanni daga gidajen jaridu dabam-dabam sun nuna ana zargin kan gwamnoni ya fara haduwa a game da ‘dan takarar shugaban kasa a APC.

Alamu na bayyana cewa wasu gwamnonin jihohin APC su na neman karkata ga mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a matsayin ‘dan takara.

Jaridar This Day ta rahoto cewa an ga gwamnoni da-dama sun yi zama da Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatan fada, Farfesa Ibrahim Gambari.

Zargin da ake yi shi ne taron da ake yi a ofishin mataimakin shugaban kasar bai rasa nasaba da yunkurin fitar da ‘dan takara ta hanyar maslaha a APC.

Gwamnonin da aka gani a Aso Villa

Rahoton da Sun ta fitar, ya ce gwamnonin da aka gani a Aso Villa daga ranar Laraba zuwa Juma’a sun hada da irinsu Dapo Abiodun da Abdullahi Sule.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika an ga fuskar Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Dr. Kayode John Fayemi da kuma su Gwamna Inuwa Yahaya da David Umahi a Aso Villa.

Osinbajo a Aso Villa
Farfesa Yemi Osinbajo a taron FEC Hoto: Laolu Akande
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta na tunanin Abdullahi Sule da Abdullahi Ganduje su na tare da Bola Tinubu, shi kuwa Dapo Abiodun yana goyon bayan Yemi Osinbajo.

Shi kuwa Kayode Fayemi yana takara, har an fara rade-radin ya janyewa Farfesa Osinbajo. Haka zalika Dave Umahi yana cikin wadanda suka saye fam.

Na san 'Yan takaran Baba

A ranar Juma’a da karfe 9:20 na dare, Bashir El-Rufai ya rubuta a Twitter, ya san wanda Muhammadu Buhari yake so a cikin ransa ya yi takara.

Yaron gwamnan na Kaduna yace labarin sirri ne, don haka ba zai iya fadawa kowa a Duniya ba.

“Ni dai na san wanda Baba Buhari yake so ya tsaida takarar shugaban kasa da na mataimakin shugaban kasa.”
“Amma kuma abin takaici, wannan ba bayanin da za a iya fallasawa ba ne, ba zan fada ba ko za a bani fam $10m.”

- Bashir El-Rufai

Gwamnoni 9 sun yi tarayya

Gwamnoni 22 APC ta ke da su a halin yanzu, kuma kusan rabinsu su na goyon bayan mulki ya bar yankin Arewa, ya koma hannun mutumin kudu a 2023.

Tun da jam’iyyar PDP ta ba ‘dan Arewa takara, sai lissafin APC mai mulki yake neman ya canza. Amma wadannan gwamnoni su na nan a kan matsayarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel