Yanzu Haka: Osinbajo Yana Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Gidansa

Yanzu Haka: Osinbajo Yana Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Gidansa

  • Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya shiga wata ganawar sirri da Shugaban jam'iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu
  • Ganawar da aka ce ana yin ta a gidan Osinbajo da ke fadar shugaban kasa a Abuja ta samu hallarcin a kalla gwamnonin jam'iyyar ta APC guda biyar
  • Wannan ganawar ta Osinbajo na shugaban na APC na zuwa ne a yayin da jam'iyyar ke tunkarar zabenta na fidda gwani na kujerar shugaban kasa a mako mai zuwa

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a halin yanzu yana ganawa da a akalla gwamnonin jam'iyyar APC guda biyar da Sanata Abdullahi Adamu shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a gidansa, rahoton Vanguard.

Yanzu Haka: Osinbajo Yana Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Ofishinsa
Osinbajo Yana Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Ofishinsa. Hoto: Vanguard.
Asali: Facebook

Taron na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin a dakin taro na Council Chambers a gidan gwamnati a ranar Talata kafin ya tafi Madrid, Spain.

Kara karanta wannan

An Zo Kaina: Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Kasar Najeriya, Tinubu

Hakan kuma na zuwa ne bayan kammala tantance yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC da kwamitin John Odigie-Oyegun ta yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da cewa a yanzu ba san ko wadanne gwamnoni ne ba, wakilin The Punch ya tabbatar cewa a ofishin mataimakin shugaban kasa ake taron.

2023: Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Kasar Najeriya, In Ji Bola Tinubu

A bangare guda, Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Sanata Bola Tinubu, a ranar Alhamis ya ce shine ya cancanci ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari saboda idan aka yi la'akari da abubuwan da ya yi a baya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai Abeokuta domin neman goyon bayan daligets gabanin zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na APC, Vanguard ta rahoto.

Jagoran na APC wanda ya yi magana cikin harshen yarbanci, ya tunatar da su irin rawar da ya taka wurin gina jam'iyyar APC har ta zama jam'iyya mai mulki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel