2023: Okorocha Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa Mafi Yawan Masu Neman Takara Suka Lale N100m Suka Siya Fom

2023: Okorocha Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa Mafi Yawan Masu Neman Takara Suka Lale N100m Suka Siya Fom

  • Rochas Okorocha, mai neman takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar APC ya bayyana dalilin da yasa wasu yan takara suka siya fom
  • Ya ce mafi yawancin masu neman takarar sun lale N100m sun siya fom din ne domin su yi amfani da hakan don neman alfarmar a basu kujerar minista idan an ci zabe
  • Jam'iyyar mai mulki ta tsayar da ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yunin shekarar 2022 don gudanar da zaben fidda gwaninta a Abuja

Daya cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Rochas Okorocha ya bayyana dalilin da yasa wasu masu neman takarar suka yi fom.

Okorocha ya bayyana cewa wasu masu neman takarar sun lale Naira miliyan 100 sun siya fom din a APC domin su nemi a musu alfarmar kujerun minista, rahoton Jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Takarar Tinubu, Osinbajo, Amaechi da Lawan a 2023 ta na raba kawunan na-kusa da Buhari

2023: Okorocha Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa Mafi Yawan Masu Neman Takara Suka Lale N100m Suka Siya Fom
Okorocha: Ainin Dalilin Da Yasa Mafi Yawancin Masu Neman Takara Suka Lale N100m Suka Siya Fom a APC. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanatan na Imo West ya ce mafi yawancin masu neman takarar suna fatan neman mukami ne daga duk wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin.

A hirar da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC a jiya Alhamis, Okorocha ya jadada cewa mafi yawancin wadanda suka siya fom din takarar shugaban kasar sun yi ne domin neman suna ko yin fice.

"Ka san cewa wasu mutane sun siya fom din takarar ne saboda su nemi alfarmar kujerar minista," in ji shi.

Ya jadadda cewa wasu daga cikin masu neman takarar shugaban kasar sun shiga takarar duk da cewa suna da tabbacin ba za su yi nasarar lashe zaben fidda gwanin ba.

An tsayar da ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yunin 2022 domin yin zaben fidda gwani a jam'iyyar ta APC mai mulki a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel