2023: Ka goya mun baya da zaran ka shiga Abuja, Tinubu ya roki wani ɗan takarar shugaban kasa
- Jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya roki gwamna Ayade kada ya goya masa baya har sai randa ya shiga Abuja
- Tinubu, ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa karkashin APC ya ziyarci Ayade ne a kokarinsa na samun tikitin APC
- Da yake jawabi, gwamna Ben Ayade, ya ce a halin yanzu lokaci ya yi mulkin Najeriya zai koma kudanci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Cross River - Tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, wanda ke fatan ya ɗare kujerar Buhari a 2023, ya roki gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya goyi bayan takararsa ta shugaban kasa.
Ayade, wanda na ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa a APC, ya gana da Tinubu ne yayin da jagaban ya kai masa ziyarsa har Kuros Riba ranar Laraba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Da yake jawabi, tsohon gwamnan Legas ɗin ya yi alkawarin haɓaka tattalin arzikin jihar Kuros Riba da zaran ya zama shugaban Najeriya.
Tinubu ya faɗa wa gwamna Ayade cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Nawa shi ne na baka girma kamar yadda kake ganin girma na, ina rokonka a matsayin babban yaya kuma wanda ya fara ayyana shiga takara, kar ka goyamun baya a yau, amma idan ka je Abuja zaka iya goya mun baya."
A wata sanarwa da Ofishin yaɗa labarai na Tinubu ya fitar, Jagoran jam'iyya mai mulki na ƙasa ya ƙara da cewa:
"Ya zama wajibi mu yi aiki tare ba wai don cigaban tattalin arzikin Kuros Riba da haɗin kan mu kaɗai ba, amma har da ƙasar mu baki ɗaya. Hakan ya rataya a kan mu saboda al'ummar mu na yanzu da jikokin mu na gaba."
Lokaci ya yi da mulki zai koma kudu - Gwamna Ayade
A nashi jawabin, gwamna Ben Ayade ya ce lokaci ya yi da kudu zata fitar da shugaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa tsarin karɓa-karɓa na nufin yi wa kowa adalci.
"Tsarin karɓa-karɓa na kunshe a cikin kundin mulkin kasa don tabbatar da daidaito, ba don kabila ko yanki-yanki ba, sai don ba kowa haƙƙinsa. Yanzu lokacin kudu ne a 2023."
A wani labarin kuma Jigon APC ya bayyana sunayen yan takara 5 da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023
Honorabul Farouk Aliyu ya ce akwai yan takarar shugaban ƙasa sama da 5 a APC da zasu iya lallasa Atiku cikin sauki a 2023.
Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya ce Atiku ba kanwar lasa bane da zasu saki jiki, zasu yi aiki tukuru don tabbatar da nasara.
Asali: Legit.ng