Rudani: Sabbin bayanai sun fito, yayin da gwamnonin APC ke shawari kan zaban magajin Buhari
- Gabanin zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, gwamnonin da aka zaba a dandalin jam’iyyar a yanzu suna neman wanda za su zaba a matsayin wanda zai gaji Buhari
- Shugaba Buhari ya yi wani taro a ranar Talata, 31 ga watan Mayu da gwamnoni, ya bukaci gwamnonin da su taimaka masa a wannan gagarumin aiki
- Sai dai taron da gwamnonin suka yi dangane da ci gaban bai haifar da wani sakamako ba, kuma sun amince za su sake haduwa a cikin wannan mako
Abuja - Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun fara neman hanyar tsayar da dan takarar shugaban kasa na bai daya bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wata majiya mai tushe a taron farko na gwamnonin ta bayyana cewa taron ya kare ne ba tare da tsayar da matsaya daya ba, inji rahoton jaridar The Punch.
Majiyar ta shaida cewa:
“Babu wata yarjejeniya tukuna. An dage taron zuwa karshen makon nan.”
Zabar dan takarar APC: Me ya faru a taron gwamnonin?
Da aka tambayi majiyar da ba a bayyana sunan ta ba a kan abin da ya faru a taron, ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Har yanzu gwamnonin suna rabe kan lamarin. Ana la'akari da abubuwa da yawa, ciki har da iyawa, yanki da addini."
Ku tuna cewa shugaban kasa a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, ya bukaci gwamnonin APC da su nemo wanda zai gaje shi daidai lokacin da ake ci gaba da tantance 'yan takarar APC.
Jigon APC: Kada ku mai da zaben fidda gwanin shugaban kasa dandalin ruwan daloli
A wnai labarin, Daily Sun ta rahoto cewa, jigon jam’iyyar APC, Mista Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi gargadin cewa kada zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya zama wani taron ruwan daloli da kuma dandalin ciniki.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa da ke Abuja, a ranar Talata, ya bayyana cewa, kasar nan ba wata kaya ce da za a yi cinikinta ba, kuma ba wata kadara ce da za a yi gwanjonta ba da sayar da ita ga mai kudi.
Ya kuma kara da cewa, ba a taba sayar da shugabancin kasa ba ba za a fara ba yanzu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng