Jam'iyyar NNPP ta baiwa Rabiu Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023

Jam'iyyar NNPP ta baiwa Rabiu Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Jam'iyya mai tashe wato NNPP mai kayan marmari ta damƙa wa Sanata Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023
  • Kwankwaso karkashin sabuwar jam'iyyar zai fafata da sauran yan takara musamman na manyan jam'iyyu PDP da APC
  • Shugaban NNPP na ƙasa, Farfesa Rufai Ahmed Alkali, ya ce sun zaɓi Kwankwaso ne bayan dogon nazari

Abuja - Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙasa ta ba tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tikitin takarar shugaban ƙasa a babban zaben 2023 da ke tafe.

Jam'iyyar ta ba Kwankwaso tikitin ne ranar Talata bayan tantance shi a babbar Sakatariyar NNPP ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Aminiya ta rahoto.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam'iyyar NNPP ta baiwa Rabiu Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake jawabi, shugaban jam'iyyar NNPP na ƙasa, Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali, ya ce sun yi dogon tunani kafin yanke hukuncin tsayar da tsohon gwamnan na Kano a matsayin wanda suke fatan ya gaji Buhari.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya shiga tsakanin shugabannin PDP bayan Atiku ya lashe tikitin takarar shugaban kasa

Baiwa Kwankwaso tikitin takara a NNPP na nufin cewa tsohon gwamnan zai fafata da yan takara musamman na manyan jam'iyyu PDP da APC a zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ban matsa dole sai na zama shugaban ƙasa ba - Kwankwaso

A watan Maris, Sanata Kwankwaso ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa NNPP, inda ya zargi babban jam'iyyar hamayyar kasar nan da zalunci da rashin adalci.

A wata hira da ya yi a kafar talabijin na Channels tv ranar Litinin, Jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya ce bai matsa dole sai ya ɗare shugabancin Najeriya ba.

"Abin da yan Najeriya ke cewa shi ne suna bukatar nagari a kowane lokaci, ni zan iya baku tabbacin cewa Ni ba mutum bane da ya matsu dole sai ya zama shugaban ƙasa."
"Mun gaji da tsohon tsarin da ake amfani da shi yau, shiyasa muka rungumi NNPP domin kawo canji, yadda abubuwa ke wakana a kasar nan yanzu ya yi muni."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya faɗi yanda ya so yamutsa zaben fidda gwanin PDP bayan sake ba Tambuwal dama

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nuna rashin jin daɗinsa da matakin barin Tambuwal ya sake jawabi har ya janye wa Atiku.

A cewar Wike , bayan ya gama jawabinsa duk bai san da janyewa ba, sai dai kaunarsa ga PDP ta sa ya zuba wa zuciyarsa ruwan sanyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel