Yan bindiga sun kashe makiyaya 4, sun sace shanaye 60 a Anambra
- Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen kudu maso gabas ta koka kan dauki dai-dai da ake yiwa mambobinta a yankin kudancin kasar
- Miyetti Allah ta ce na baya-bayan nan ya afku a jihar Anambra ne inda yan bindiga suka kashe mata mutane hudu sannan suka sace masu shanaye 60
- Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Soludo da hukumomin tsaro a kan su dauki matakin gaggawa don kawo karshen lamarin
Anambra - Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen kudu maso gabas ta bayyana cewa yan bindiga sun kashe mata mambobinta hudu a jihar Anambra a ranar Litinin, sannan sun sace masu shanaye 60.
A wata sanarwa da ya gabatarwa manema labarai a Awka, jihar Anambra, shugaban kungiyar a yankin, Alhaji Gidado Sidikki, ya ce an kai harin ne a sansanin Fulani da ke garin Ndukwenu, karamar hukumar Orumba ta arewa a jihar, Daily Trust ta rahoto.
Sidikki ya bayyana sunayen mamatan a matsayin Mohammed Idris, Sale Idris, Abdulmumkni Idris da Musa Idris.
Ya kuma bayyana cewa an gano gawarwakin Mohammed da Sale yayin da har yanzu ba a ga na sauran mutane biyun ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto, sanarwar ta ce:
“Ana yawan kashe mambobinmu ba tare da sun aikata wani laifi ba; ba mu san laifin da muka aikata ba a jihar Anambra.
“Yayin da muke godiya ga gwamnatin jihar karkashin Farfesa Chukwuma Charles Soludo da hukumomin tsaro, muna kira ga a gaggauta daukar mataki don dakatar da kashe-kashen mutanenmu. A yanzu bama iya tafiya hankali kwance a jihar.”
"Mutane 4 da aka kashe sune; Mohammed Idris, Sale Idris, Abdulmumini Idris da Musa Idris.
“A yanzu haka, an gano gawarwakin Mohammed Idris da Sale Idris yayin da sauran mutane 2 ba'a gansu ba.”
Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce bai riga ya samu rahoton harin ba.
Yan bindiga sun sace mutane da yawa, sun kona motoci a wani kazamin hari da suka kai babbar hanyar Kaduna
A wani labarin kuma, ttsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama bayan sun farmaki matafiya a hanyar babban titin Kaduna-Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigar sun toshe babbar hanyar a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, sannan a cikin haka suka kona motoci takwas, Channels Tv ta rahoto.
An tattaro cewa bayan nan maharan sun yi awon gaba da wasu adadi na matafiya wanda mafi yawansu mata da yara ne zuwa wani waje da ba a sani ba.
Asali: Legit.ng