Shugabannin PDP sun dare gida biyu kan zaɓen mataimakin Atiku a zaɓen 2023

Shugabannin PDP sun dare gida biyu kan zaɓen mataimakin Atiku a zaɓen 2023

  • Bayan nasarar Atiku a zaɓen fidda gwanin PDP, batun nemo wanda zai zama mataimaki ya raba kawunan shugabannin jam'iyya
  • Wata majiya ta bayyana cewa bangaren kwamitin gudanarwa NWC da kuma BoT na kokarin kawo wanda suke so daban-daban
  • Gwamna Wike na jihar Ribas na ɗaya daga cikin mutanen da ake tsammanin PDP ka iya jawo wa zuwa matakin na mataimaki

Abuja - Batun wanda zai zama abokin takara wato mataimaki ga Alhaji Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa da PDP ta tsayar a zaben 2023, ya ɗauki sabon salo.

Daily Trust ta tattara cewa jam'iyyar PDP tare da haɗin guiwar ɗan takaran sun shirya wasu matakai da zasu taimaka wajen zakulo abokin takara wanda masoyan PDP da yan Najeriya zasu karɓe shi hannu biyu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

Atiku Abubakar wazirin Adamawa.
Shugabannin PDP sun dare gida biyu kan zaɓen mataimakin Atiku a zaɓen 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyar ta kara da cewa kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa karkashin shugaba, Dakta Iyorchia Ayu, da kwamitin amintattu (BoT) karkashin Sanata Walid Jibrin suna kokarin cusa mutane daban-daban.

Shugaban BoT, Sanata Walid Jibrin, a wata sanarwa ya ce kwamitinsa a shirye yake ya taimakawa wa ɗan takara wajen zakulo amintaccen mataimaki daga yankin kudancin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban BoT ya ce:

"BoT zata taimaka wa Jam'iyya da kuma wazirin Adamawa shi kansa domin zaƙulo amintaccen mataimakin shugaban ƙasa daga yankin kudancin Najeriya."

BoT ta yi hannun riga da kwamitin NWC

Amma majiyar ta ƙara da cewa taimakon da BoT ta shirya ba da wa ka iya yin hannun riga da tsarin kwamitin gudanarwa NWC wanɗan da ke kokarin jan ragamar ɗakko wanda zai takara da Atiku a 2023.

Gwamna Wike na jahar Ribas shi ne ya zo na biyu a bayan Atiku Abubakar da kuri'u 237 kuma yana daga cikin mutanen da ake hasashen ba mukamin.

Kara karanta wannan

Rochas Okorocha, Lawan da sauran yan takarar shugaban ƙasa 9 da Kwamitin APC zai tantance yau

A wani labarin kuma Gwamnonin APC sun sa labule bayan Buhari ya faɗa musu matsayarsa kan wanda zai gaje shi a 2023

Bayan shugaban ƙasa Buhari ya gaya musu matsayarsa kan wanda zai gaje shi, yanzu haka gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri.

A dazu ne kafin ya tafi Spain, Buhari ya faɗa wa gwamnonin cewa yana bukatar goyon bayansu wajen zakulo wanda zai gaje shi a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262