Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri bayan Buhari ya faɗa musu matsaya kan wanda zai gaje shi

Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri bayan Buhari ya faɗa musu matsaya kan wanda zai gaje shi

  • Bayan shugaban ƙasa Buhari ya gaya musu matsayarsa kan wanda zai gaje shi, yanzu haka gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri
  • A dazu ne kafin ya tafi Spain, Buhari ya faɗa wa gwamnonin cewa yana bukatar goyon bayansu wajen zakulo wanda zai gaje shi a 2023
  • Buhari ya bayyana irin abubuwan da zai duba ya zaɓi ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa 25 na APC

Abuja - Gwamnonin da suka ɗare madafun iko karkashin inuwar APC sun shiga ganawar sirri yanzu haka a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa ana tsammanin gwamnonin zasu maida hankali kan matsayar shugaban ƙasa Buhari na cewa yana son ya zabi wanda zai gaje shi.

Gwamnonin APC.
Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri bayan Buhari ya faɗa musu matsaya kan wanda zai gaje shi Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Wasu bayanai da jaridar ta tattara ya tabbatar da cewa har zuwa misalin ƙarfe 5:00 na yamma gwamnonin ba su fito daga ɗakin taron ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya faɗa mana ɗan takarar da yake son ya gaje shi a 2023, Gwamnan arewa ya fasa kwai

Da yammacin Talata, Shugaba Buhari, ya gaya wa gwamnonin jam'iyyar APC yayin ganawarsu, cewa yana son su goya masa baya ya zaɓi wanda zai gaje shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya ce:

"Domin cigaba da tsarukan cikin gida da APC ta ɗakko da kuma lamarin babban taro da muke fuskanta nan da yan kwanaki, ina bukatar goyon bayan gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki wajen zaɓar wanda zai gaje ni."
"In zaɓi wanda zai ɗaga tutar jam'iyyar mu a zaɓe har zuwa cikin ofishin shugaban ƙasan tarayyan Najeriya a 2023."

A wurin taron, shugaban ƙasan ya bayyana abubuwan da zai kalla kafin ya zaɓi ɗaya daga cikin yan takara kuma ya goya masa baya daga cikin yan takara 25.

Buhari ya tafi Spain bayan taronsa da gwamnonin APC

Jim kaɗan bayan ganawarsa da gwamnonin, Shugaba Buhari ya kama hanyar zuwa ƙasar Spain a nahiyar turai, inda ya bar gwamnonin su ƙara tattaunawa kan matsayarsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya ce zai zaɓi wanda zai gaje shi a 2023, ya nemi goyon bayan gwamnoni

A wani labarin kuma mun kawo muku cewa Hukumar INEC ta soke amfani da wani muhimmin Fom a zaɓen 2023

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta soke amfani da Fom ɗin 'rahoton abun da ya faru' a dukkan zaɓukan Najeriya.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shi ne ya bayyana haka a Ado Ekiti, ya ce ba za'ai amfani da Fom din a zaɓen Ekiti ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel