Shirin 2023: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin APC kan zaben magajinsa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC gabanin zaben fidda gwanin shugaban kasa a APC
- Ana kyautata zaton shugaban zai tattauna da gwamonin ne kan batutuwa da suka shafi tsayar da dan takarar shugaban kasa na APC
- Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana abubuwan da ke gudana a cikin taron ba da ya samu halartar jiga-jigan siyasar APC
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yanzu haka yana ganawa da gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki.
An tattaro cewa, taron ana yin sa ne kan batun zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da za a yi a ranakun Talata da Laraba a mako mai zuwa.
Dukkan gwamnonin jam’iyyar APC sun halarci taron kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.
Taron wanda ke gudana a zauren majalisar dokokin kasa ya samu halartar shugaban jam'iyyar na kasa Abdullahi Adamu da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dukkan ‘ya’yan kungiyar gwamnonin masu ci gaba daya sun hallara sai Nasir El-Rufai na Kaduna wanda mataimakiyarsa Hadiza Balarabe ta wakilta, rahoton Punch.
Ganawar ta Buhari da gwamnonin APC ta zo ne daidai lokacin da jam'iyyar ta APC ke ci gaba da tantance 'yan takararta a shirin zaben fidda gwani.
tuni dai dama jam'iyyar ta tantance wasu jiga-jigan da suka sayi fom din takarar jam'iyyar, inda za ta ci gaba da tantance sauran a yau Talata.
Tinubu: Babu wani cin girma da zan yi, burina kawai na yi takara a zaben 2023 mai zuwa
A wani labarin na daban, rahotanni sun bayyana cewa Bola Tinubu ya dage kan cewa ba zai janye daga takara ba duk kuwa abin da zai faru.
An ce dan takarar na kan gaba a jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Jaridar Leadership ta yi ikirarin cewa Tinubu ya bayyanawa kwamitin cewa ba zai amince da wata matsaya da za a zo da ita kan 'yan takara ba.
Asali: Legit.ng