Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

  • Samuel Ohubunwa, mai neman takarar shugaban kasa na PDP daga Jihar Abia ya nuna takaicinsa kan yadda daliget din jiharsa ba su zabe shi ba
  • Ohubunwa, wanda ya samu kuri'a daya tak a zaben fidda gwanin ya ce daliget din sun zabi kudi ne a maimakon cancanta
  • Masanin kimiyyan magungunan ya bayyana cewa bada cin hanci a siyasa ya zama al'ada amma dole a taru a yi yaki da shi domin ba abu bane mai kyau

Mai Neman Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar PDP, Samuel Ohubunwa, ya nuna takaicinsa kan yadda daliget din jiharsa suka ki jefa masa kuri'a a zaben fiddda gwani na shugaban kasa na PDP da jam'iyyar ta yi a ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

Daily Trust ta rahoto ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana kan zaben fidda gwanin na shugaban kasa a shirin Channels TV a safiyar ranar Litinin.

Na Ji Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP
'Dan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP: Na Ji Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jihar Abia, wata ita jihar da dan siyasar ya fito, tana da daliget 17 amma kuri'a daya tak ya samu a zaben da aka yi a Moshood Abiola Stadium a Abuja.

Ohuabunwa ya ce: "Ina tunanin wadanda za su zabe ni za su fi hakan daga jiha ta."

Daliget sun fifita kudi a kan cancanta, Ohuabunwa

Kwararren a bangaren kimiyyan magunguna ya ce ya yi takaicin ganin yadda daliget din suka yi zabe saboda kudi a maimakon cancanta, Information Nigeria ta rahoto.

Ya ce:

"Daya daga cikin ciyamomin ya ce da ni 'Mazi' abin da ka fada da hanyar da za ka bi ita ce dai-dai. Ba za ka iya kawo gyara Najeriya ba idan kana daga waje. Tafi ka nemi kudi duk inda ya ke. Ka kira ni idan ka samu. Dole sai kana daga ciki za ka iya kawo canji."

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Ya ce an mayar da bada cin hanci tamkar al'ada a siyasar Najeriya yana mai cewa abin dauki lokaci kafin a canja.

"Da na shiga takarar, na ce ba zan siya abin sha ba, ba zan bada kudin zirga-zirga ba.
"Za ka zo taro amma mutane za su tashi su fita su bar ka. Sun ce ban shirya ba.
"Na fara yaki da wannan al'adar a wani lokaci, zabi ne mai wahala," in ji Ohuabunwa.

Ya ce kashe kudi mai yawa don kana son yi wa al'ummar ka hidima bai dace da fahimtarsa ba, 'amma shine al'adar.'

Ya ce rashawa ya zama ruwan dare kuma ba boyayyen abu bane kuma ya kamata a yake shi.

Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC

A wani rahoton, dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya bayyana dalilinsa na barin inda ake zaben fidda gwanin jam’iyyar APC, kuma ya kalubalanci sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

Sharada ne dan takara daya da ya nuna rashin amincewarsa akan gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna a farkon watan Mayu, rahoton The Cable.

A wata takarda wacce Daily Nigerian ta saki ranar Juma’a, Sharada ya ce dakyar shi da wasu mabiyansa su ka sha daga harin da aka kai musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164