Tsohon dan takara a PDP ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour
- Bayan ficewa daga jam'iyyar PDP gabanin zaben fidda gwani, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour, ya samu tikitin takara
- Ya samu tikitin gwabzawa da 'yan takara a sauran jam'iyyu a 2023 ne bayan da Pat Utomi ya janye daga takara
- Jam'iyyun siyasa na ci gaba da gudanar da zabukan fidda gwani a kasar nan yayin da ake shirye-shiryen zaben 2023
Delta - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya karbi tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, rahoton jaridar Punch.
Hakan na zuwa ne bayan da wani dan takarar shugaban kasa a dandalin jam’iyyar, Farfesa Pat Utomi, ya amince da marawa Obi baya, wanda ya koma jam’iyyar a makon jiya.
Utomi, wanda fitaccen farfesa ne a fannin tattalin arziki, ya yanke amincewa janyewa Obi a ranar Litinin a wurin da aka gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar a Delta.
Sai dai SaharaReporters ta samu labarin cewa Utomi ne ya taka rawar gani wajen ganin Obi ya koma jam’iyyar Labour daga PDP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Utomi ya sanar da cewa Obi matashi ne mai fafutuka tare da ikon aiwatar da canjin da ake bukata a tsarin Najeriya.
Har ila yau, wani dan takarar mai shekaru 45, Joseph Faduri ya janyewa tsohon gwamnan duk dai a wurin zaben fidda gwanin.
Obi wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya fice daga jam’iyyar sannan kuma ya fice daga takarar shugaban kasa a dandalin jam’iyyar a ranar 25 ga watan Mayu.
APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce
A wani labarin na daban, Godday Odagboyi, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Apa/Agatu, ya sha kaye a yunkurinsa na sake tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa, TheCable ta ruwaito.
Odagboyi wanda ya tsaya takarar neman tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun Adama Adama, hamshakin dan kasuwa wanda aka fi sani da Otalaka.
Da yake sanar da sakamakon a ranar Asabar, shugaban kwamitin zabe Franklin Shagbaor, ya ce Adama ya samu kuri’u 21,747 inda ya doke Odagboyi wanda ya samu kuri’u 3,151.
Asali: Legit.ng