Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki
- Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Borno na 2023, Mohammed Jajare, ya zargi gwamnatin Babagana Zulum da son kai
- Jajare wanda ya sha alwashin sauke Zulum daga kan kujerar, ya ce gwamnan na baiwa yan uwa da abokai kwangiloli
- Ya kuma zargi gwamnatin APC da siye manyan jiga-jigan PDP don mayar da jihar tsarin jam'iyya daya
Borno - Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic party (PDP) a zaben gwamnan jihar Borno na 2023, Mohammed Jajare, ya zargi gwamnan jihar, Babagana Zulum na baiwa abokai, iyalai da yan uwansa kwangiloli ta hanyar fakewa da aiki kai tsaye.
Jajare ya kuma yi zargin cewa gwamnan na siye manyan yan PDP a jihar don kawar da adawa a jihar.
Da yake zantawa da jaridar The Punch a ranar Lahadi, Jajare ya bayyana cewa tsawon shekaru gwamnati mai ci a Borno ta fitar manyan masu fada aji daga PDP don ci gaba da tsarin jam’iyya daya a jihar.
Ya ce da wannan zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP da aka yi cikin gaskiya da amana wanda ya samar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin gwaninta, jam’iyyar za ta tabbatar da sukar manufofin gwamnatin APC idan ba zai amfani mutanen Borno kamar yadda yake a kundin tsarin mulki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
“Da farko za mu kaucewa duk wasu tsare-tsare na APC, za mu gabatar da ainahin adawa a jihar Borno. Za mu soki manufofinsu da basu da kyau. Za mu tattauna da kuma tara jama’a sannan mu wayar masu da kai a yawancin manufofin da suke yi kuma za mu yi mahawara kan duk wata manufa da bata da kyau ga mutanen jihar Borno kafin ya faru.
“Jam’iyya mai mulki ce ta haifar da duk wani rabuwar kai da rashin fahimta a PDP. PDP na da karfi a Borno. Jam’iyyar mai mulki ce ta saka ra’ayi a PDP wanda yasa ‘ya’yan jam’iyyar ke fada da junansu.
“Manufar APC a jihar shine ta siye manyan PDP da nufin mayar da jihar ta jam’iyya daya. Sun siye dukkanin manya daga PDP don murkushe jam’iyyar sannan duk wani babba da baya cikinsu za a matsa mai har sai ya bar jihar.”
Ya ce idan aka zabe shi a matsayin gwamna a 2023, zai dawo da dukkanin ma’aikatan gwamnati da aka sallama sannan ya biya su hakkinsu da aka tauye tsawon shekaru.
A cewarsa, yanayin rashin tsaro a jihar ya kawo wahalhalu da bai kamata ace an yanke ma’aikata daga inda suke samun kudin shiga ba bayan an hana su zuwa gonaki.
Jajare ya ce:
“Har yanzu rashin tsaro barazana ce ga jihar Borno. Idan aka zabe ni a matsayin gwamna, za a dawo da dukkanin ma’aikatan gwamnati da aka sallama bakin aikinsu sannan a biya su cikakken albashinsu na baya.
“Kamfanoni masu kima ne ya kamata a dunga baiwa kwangiloli bawai yan uwa da abokai ba da sunan aikin kai tsaye amma kowa ya san ba aiki kai tsaye bane. Kwangila ne ake baiwa abokai, yan uwa da hadimai wanda yawancinsu ba a yinsu yadda ya kamata kuma suna lalacewa cikin dan kankanin lokaci.”
Dan takarar gwamnan APC ya fice daga jam’iyyar, ya ce sai ya yi takara a 2023
A wani labarin, Cif Adebayo Adelabu, wanda aka fi sani da Penkelemes, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da wasu fusatattun shugabannin jam’iyyar.
Adelabu ya kasance dan takarar gwamna na APC a 2019 amma ya sha kaye a hannun Sanata Teslim, Folarin a zaben fidda gwanin jam’iyyar na 2023 da aka kammala kwanan nan.
Wasu shugabannin APC a Oyo da Adelabu sun sanar da sauya shekarsu a ofishin kamfen din Adelabu da ke Ibadan, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng