Yan Daba Suka Hana Daliget Ɗina Zaɓe: Tsohon Hadimin Buhari, Bashir Ahmed Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓe a Kano

Yan Daba Suka Hana Daliget Ɗina Zaɓe: Tsohon Hadimin Buhari, Bashir Ahmed Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓe a Kano

  • Bashir Ahmad, tsohon hadimin Shugaba Buhari, bayan shan kaye a zaben fidda gwani na dan majalisar tarayya a Kano ya ce bai yarda da sakamakon zaben ba
  • Bashir ya yi ikirarin cewa 'yan daba sun hana shi da daliget dinsa shiga wurin zaben don haka galibinsu ba su jefa kuri'a ba, ya nemi a sake sabon zabe kuma wannan karon kada a yi magudi
  • Tsohon hadimin shugaban kasar ya mika godiyarsa ga magoya bayansa da daliget dinsa da sauran masu masa fatan alheri inda ya bukaci su kwantar da hankulansu su cigaba da bin doka da oda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bashir Ahmad, tsohon hadin Shugaba Muhammadu Buhari a bangaren sabbin hanyoyin watsa labarai kuma mai neman takarar dan majalisa na mazabar Albasu/Gaya/Ajingi a Kano ya yi watsi da zaben fidda gwani da aka yi a ranar 27 ga watan Mayu.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar 28 ga watan Mayu, Bashir ba zai amince da sakamakon zaben ba domin abubuwan da suka faru a wurin zaben sun janyo cikas na inganci da nagartan zaben, kuma idan ya yi shiru bai yi wa mutanensa da jam'iyyar APC adalci ba.

'Yan Daba Sun Hana Daliget Ɗina Zaɓe: Tsohon Hadimin Buhari, Bashir Ahmed Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓe a Kano
Tsohon Hadimin Buhari, Bashir Ahmed Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓe a Kano, Ya Ce Magudi Aka Tafka Masa. Hoto: Bashir Ahmad.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan daba sun hana ni shiga wurin zabe, sun hana mafi yawancin deliget dina kada kuri'a - Bashir Ahmad

A cewarsa, an hana mafi yawa cikin daliget dinsa shiga wurin zaben ballantana su kada kuri'arsu, sannan babu wata takardan zabe dauke da sa hannun wakilansa don ba a bari ma sun shiga wurin zaben ba.

"Da isa na wurin zaben a matsayin mai neman takara, an hana ni zuwa wurin zaben. Magoya baya na da ke harabar sun ki amincewa da rashin adalcin suka dage sai an bari na shiga.

"Kamar yadda na saba fada, bana fatan wani ya rasa ransa ko ya jikkata saboda wata bukata nawa, don aka a lokacin na yanke shawara abin da ya fi dacewa shine in bar don hankula su kwanta da kuma kiyaye lafiyar mafi yawancin daliget dina, wakilai da magoya baya da yan daba ke yi wa barazana," wani sashi cikin rubutun da ya wallafa.

Bashir ya nemi a sake shirya sabon zabe da za a gudanar cikin adalci

Daga karshe, Bashir ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC, su ceto mutuncin jam'iyyar ta hanyar umurtar yan kwamitin zabe su sake shirya sabon zabe da za a yi adalci.

Ya kuma mika godiyarsa ga magoya bayansa, daligets da bisa jajircewarsu duk da barazanar da aka yi musu, sannan ya bukaci su cigaba da biyayya ga doka da oda.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel