Tikitin shugaban kasa na PDP: Ina addu’a Allah yasa Wike ya kai labari – Okezie Ikpeazu
- A yau Asabar, 28 ga watan Mayu ne jam'iyyar PDP ke gudanar da zaben fidda dan takararta na shugaban kasa
- Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya bayyana cewa yana nan yana addu'a don ganin takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi nasara a zaben
- Wike dai yana tseren tikitin ne da gogaggun yan siyasa irin su Atiku Abubakr, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal, Bala Mohammed da sauransu
Abuja - Yayin da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara babban taronta na kasa a yau Asabar, 28 ga watan Mayu, gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya bayyana cewa yana son gwamnan jihar Abia, Nyesom Wike ya kai labari.
Ikpeazu ya bayyana haka ne a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, jaridar Vanguard ta rahoto.
Batun fitar da dan takarar maslaha ya rushe: Atiku, Saraki da sauran yan takarar PDP sun ce sai an fafata
Jam’iyyar adawar na da kimanin yan takara 15 da ke neman tikitin takarar shugabancin kasar.
Da wannan, Wike zai fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon shugaban Majalisar dattawa, Pius Anyim Pius.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai gwamnan jihar Cross River, Emmanuel Udom, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da sauransu.
Da yake amsa tambayoyi kan wanda zai lashe zaben Okezie ya ce:
“Gwamna Wike nake tsammani. Adduo’ina na tare dashi.
“Kun ga, muna bukatar mutum da zai iya kare mai kudi da talaka. Mutum da zai kare mutane. Muna bukatar mutum da zai iya daidai tattalin arziki.”
Ba mu dage zaben fidda dan takarar shugaban kasa ba - PDP
A wani labarin, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata batun dage babban taronta da aka shirya gudanarwa a yau Asabar, 28 ga watan Mayu.
Zaben fidda dan takarar PDP: An gano fostocin Hayatu-Deen baje a wajen taron duk da janyewa daga tseren
Gabannin babban zaben 2023, deleget din PDP sun taru a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar inda ake sanya ran taron zai gudana.
Akwai rahotannin cewa babbar jam’iyyar adawar kasar na iya dage zaben fidda dan takararta na shugaban kasa, awanni bayan jam’iyyar APC ta mayar da nata zuwa 6 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng