Shugabancin Kasa Na 2023: Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Wani Shahararren Attajirin Ɗan Kasuwa

Shugabancin Kasa Na 2023: Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Wani Shahararren Attajirin Ɗan Kasuwa

  • Dan takarar shugaban kasa kuma tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ya na ci gaba da samun goyon baya yayin da zaben 2023 ke matsowa
  • Wani fitaccen dan kasuwa, Mogaji Bowale Oluwale Arisekola ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ke da damar sauya Najeriya
  • A ranar Juma’a, 27 ga watan Mayun 2022, Mogaji ya ce yana bayan Tinubu dari bisa dari, kuma ba ya da niyyar yin jayayya da abokatarsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya samu goyon baya daga wani fitaccen hamshakin dan kasuwa, Mogaji Bowale Oluwale Arisekola.

Kamar yadda Jaridar New Telegraph ta ruwaito, Mogaji ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Mayu a Abuja, yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a NNPP Ya Sallama Wa Kwankwaso, Amma Ya Nemi Wata Alfarma Daga Wurin Kwankwason

Shugabancin Kasa Na 2023: Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Wani Shahararren Attajirin Ɗan Kasuwa
2023: Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Wani Shahararren Attajirin Ɗan Kasuwa. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mogaji ya kwatanta Tinubu a matsayin dan takarar da ya fi cancantar shugabancin kasa don bunkasa Najeriya da fitar da ita daga halin da ta ke ciki.

Kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, Mogaji ya ce shi amintaccen Tunubu ne kuma zai ci gaba da kasancewa hakan.

Tunatarwar da Mogaji yayi akan mulkin Tinubu lokacin yana gwamnan Legas

Yayin da Mogaji ya ke bayani akan goyon bayansa ga Tinubu, ya bayyana ayyukan da ya yi lokacin ya na gwamnan Legas, inda ya ce:

“Tsohon gwamnan Legas din ya kawo kirkire-kirkire a gwamnatin jihar yayin da ya kwashe shekaru takwas yana kan karagar mulki, ina mai tabbatar muku, zai yi makamancin hakan idan ya zama shugaban kasar Najeriya.
“Ban ki goya masa baya ba kuma ki nuna goyon bayan a gaban mutane ba. Na yarda da cewa, ba tare da zargi ba, zai samar da ingantaccen mulki don fitar da Najeriya daga kangin da ta ke ciki.”

Kara karanta wannan

Lamidon Adamawa ya bukaci Musulmai da su ji tsoron Allah

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164