Da Dumi-Dumi: Shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawa ya yi murabus

Da Dumi-Dumi: Shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawa ya yi murabus

  • Bayan janye wa daga shiga zaɓen fidda gwanin PDP, Sanata Abaribe ya sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP baki ɗaya
  • Haka nan kuma sanatan ya aike da wasika ga shugaban majalisar dattawa yana mai sanar masa ya aje mukamin shugaban marasa rinjaye
  • Ya ce ya ɗauki wannan matakin sabida rashin adalcin PDP da kuma yi wa doka hawan kawara

Abia - Rahoton da muke samu yanzun ya nuna cewa, Sanata Enyinnaya Abaribe ya fice daga babbar jam'iyyar hamayya ta kasar nan PDP, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sanata Abaribe ya kuma yi murabus daga muƙaminsa na shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan ƙasar nan.

Idan zaku iya tunawa Sanatan ya janye daga shiga zaɓen fitar da ɗan takarar gwamnan Abia na jam'iygar PDP, wanda ya gudana ranar Laraba da ta gabata, kwana biyu da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

Karin bayani: APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a bauchi

Sanata Abaribe daga jihar Ribas.
Da Dumi-Dumi: Shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawa ya yi murabus Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya tabbatar da ficewa daga PDP da kuma murabus daga kujerar shugaban marasa rinjaye a wasu wasiku daban-daban da ya aike wa shugaban PDP na gundumarsa dake karamar hukumar Obingwa, jihar Abia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma ya aike da kwafin waɗan nan takardu ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.

Sanatan ya ƙara da cewa ya dauki matakin ficewa daga PDP ne saboda karya doka da rashin sanin ya kamata wajen yanke hukunci kan harkokin jam'iyya.

Wani sashin takardan ya ce:

"Na rubuto wannan takarda ne domin sanar da ku shawarin da na yanke na yin murabus daga mamban jam'iyyar PDP. Hakan ya zama wajibi duba da abun da ya fito fili na saba doka da rashin demokaradiyya a harkar tafiyar da jam'iyya."

Abaribe ya aje mukamin shugaban marasa rinjaye

A ɗaya wasikar da ya aike wa shugaban majalisar Dattawa, Sanata Abaribe ya sanar wa abokan aikinsa cewa ya bar PDP kuma hakan na nufin ya aje mukamin shugaban marasa rinjaye.

Kara karanta wannan

Kafin tafiya Malabo, Buhari ya gana da gwamnonin APC kan wanda jam'iyya zata tsayar ya gaje shi a 2023

Wasi sashin takaradar da Punch ta ruwaito ya ce:

"Ina mai sanar maka da sauran mambobin majalisar dattawa cewa na fice daga jam'iyyar PDP ta hanyar mazaɓa ta, kuma hakan na nufin na yi murabus daga shugaban marasa rinjaye."

Wace jam'iyya Sanatan ya koma?

A ranar Jumu'a 27 ga watan Mayu, 2022, Sanata Abaribe ya tabbatar wa jaridar Vanguard a Umuahia cewa ya shiga jam'iyyar APGA kuma zai nemi komawa majalisar Dattawa a 2023.

Tun a ranar lahadi, shugabannin jam'iyyar APGA suka ziyarci Sanatan inda suka roke shi da sauran tawagarsa su shigo jam'iyyarsu.

APGA ta yi wa Abaribe alƙawarin tikitin takarar Sanata kyauta, amma ya buƙaci su ba shi lokaci ya yi shawara da mutanen mazaɓarsa da abokan siyasa.

A wata hira da walikin jaridar, Abaribe ya ce ya riga ya yanke hukuncin komawa APGA, inda ya ƙara da cewa da shi za'a fafata a zaɓen fidda gwani na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

Bisa haka, Abaribe zai gwabza da gwamna Okezie Ikpeazu, wanda jam'iyyar PDP ta tsayar a kujerar ta sanata.

A wani labarin kuma kafin tafiya Malabo, Buhari ya gana da gwamnonin APC kan wanda jam'iyya zata tsayar ya gaje shi a 2023

Shugaban ƙasa Buhari ya gana da gwamnoni kan batun da ya shafi zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da ke tafe.

Wasu bayanai sun nuna cewa shugaban bai bayyana wa kowa wanda yake so ba, ya umarci a gudanar da sahihin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel