Karin bayani: APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a bauchi

Karin bayani: APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a bauchi

  • Jam'iyyar APC ta kammala zaben fidda gwanin gwamna a jihar Bauchi, deliget sun zabi dan takarar gwamna na gaba
  • An sanar da sunan tsohon shugaban hafsun sojin sama a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a zabe mai zuwa
  • Jihohi na ci gaba da tattara sakamakon zaben fidda gwani, kana ana fitar da sunayen 'yan takarar da suka lashe zabe

Bauchi - Rahoton da muke samu daga Punch ya ce, an bayyana tsohon shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Abubakar Saddique a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar APC.

Sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan kammala kada kuri'u da deliget-deliget na APC suka yi a zaben fidda gwanin da ya gudana a jihar.

Tsohon shugaban hafsan sojin sama ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan APC a Bauchi
Da Duminsa: Tsohon hafsan sojin sama ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan APC a Bauchi | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ana ci gaba da gwabza zabukan fidda gwanin gwamnonin jam'iyyar APC a jihohi, kuma sakamako ya fara fitowa tuntuni.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Umar Bago ya lashe zaben fidda dan takarar gwamnan APC a Neja

Sakamakon zaben fidda gwanin gwamnan APC a Bauchi

Tsohon jami’in sojan saman ya samu kuri’u 370 inda ya doke wasu ‘yan takara hudu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban abokin hamayyarsa, Halliru Jika, Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya samu kuri’u 278, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Nura Manu ya samu kuri’u 269, Musa Babayo ya samu kuri’u 70, yayin da Mahmud Maijama’a ya samu kuri’u 8. Muhammed Pate bai cisamu kuri'a ko daya ba.

Abubakar ya yi aiki a matsayin babban hafsan sojin saman Najeriya daga ranar 13 ga Yuli, 2015, zuwa 26 ga Janairu, 2021.

Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki

A wani labarin na daban, yayin da ake tsaka da zaben fidda gwanin jam’iyyar APC a Jihar Sokoto, akalla ‘yan takarar gwamna guda uku cikin guda 5 ne su ka bar wurin zaben, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda wasu Gwamnonin jihohi su ka yi kutun-kutun har sai da Peter Obi ya hakura da PDP

Hakan ya biyo bayan rashin wutar lantarki a babban ofishin jam’iyyar na jihar bayan man fetur din injin da ke samar da wutar ya kare.

Wakilin The Punch ya bayyana yadda lamarin ya kai kusan sa’a daya inda wasu ‘yan takarar su ka nemi a dakata da zaben har a dawo da wuta amma aka ki sauraronsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel