Shugaba Buhari ya gana da gwamnonin APC kan wanda jam'iyya zata tsayar ya gaje shi a 2023

Shugaba Buhari ya gana da gwamnonin APC kan wanda jam'iyya zata tsayar ya gaje shi a 2023

  • Shugaban ƙasa Buhari ya gana da gwamnoni kan batun da ya shafi zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da ke tafe
  • Wasu bayanai sun nuna cewa shugaban bai bayyana wa kowa wanda yake so ba, ya umarci a gudanar da sahihin zaɓe
  • A ranar Lahadi da kuma Litinin masu zuwa Deleget ɗin APC zasu raba gardama kan wanda jam'iyya zata ba tutar takara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gabanin zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban kasa na APC, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnonin jam'iyya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa shugaban ƙasan ya sa labule da gwamnonin APC ne ranar Talata da daddare.

Bayanai sun nuna cewa taron ya maida hankali ne kacokan wajen tattaunawa kan abun da ya shafe zaben fitar da ɗan takarar shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari ya gana da gwamnonin APC kan wanda jam'iyya zata tsayar ya gaje shi a 2023 Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Jam'iyya mai mulki ta zaɓi ranar Lahadi da Litinin domin gudanar da zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, inda wakilan jam'iyya wato Deleget zasu raba gardama kan wanda APC zata ba tuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Damuwa ta shiga zukatan yan takarar shugaban ƙasa 23 na APC, sakamakon rashin tabbbas wajen tantance su, wanda aka tsara yi ranar Litinin daga baya aka ɗaga sai baba ta gani.

Wata majiya da ke kusa da jam'iyya, gwamnoni da yan takarar shugaban kasa ta ce dukkan su na jiran zaɓin shugaba Buhari ne gabanin zaɓen fid da gwani.

Ɗaya ɗaga ciki, wani tsohon gwamna ya ce:

"Tashin hankali da ruɗanin da ke cikin jam'iyya shi ne rashin tsoma bakin shugaban ƙasa, kowa ya shiga rudani."

Abinda Buhari ya faɗa wa gwamnoni

Wata majiya kusa da Buhari ya faɗa wa wakilin jaridar cewa an umarci gwamnoni da shugabannin jam'iyya su tabbatar da sun gudanar da sahihin zaɓe.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani gwamna ya lashe zaben fidda gwanin APC, zai nemi tazarce a 2023

Ya ce:

"Shugaban ƙasa ya faɗa wa gwamnoni da jam'iyya cewa su tabbatar an yi zaɓe sahihi, bai faɗi sunan kowa ba game da zaɓinsa a wurin taron."

A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Zamfara ya janye karar da ya maka APC da Matawalle

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, ya ba da umarnin gaggawa na janye kara uku da ya shigar da shugabancin jam'iyyar APC.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan sulhun da aka yi tsaganin ɓangarorin APC biyu na Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel