Yadda wasu Gwamnonin jihohi su ka yi kutun-kutun har sai da Peter Obi ya hakura da PDP

Yadda wasu Gwamnonin jihohi su ka yi kutun-kutun har sai da Peter Obi ya hakura da PDP

  • Ana zargin gwamnonin kasar kudu maso gabas sun taimakawa jam’iyyar PDP wajen rasa Peter Obi
  • Peter Obi ya fice daga PDP ne kwatsam ana shirin zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasan 2023
  • Gwamnonin yankin da ya fito sun ki mara masa baya, su na neman karbe wurinsa a wajen Atiku

Bayanai sun fito a game da rawar da wasu gwamnonin jihohin PDP su ka taka wajen ganin Peter Obi ya fice daga jam’iyyar gabanin zaben 2023.

Vanguard ta rahoto cewa akwai gwamnonin jam’iyyar adawa da suka tasa Peter Obi da kulli da kutun-kutun, a sanadiyyar wannan ya canza gida.

A zaben 2019, Mista Obi ne ya tsaya a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: Jerin gwamnoni da mataimakan gwamnoni da suka lashe tikitin majalisar dattawa

A zaben, Atiku Abubakar ya samu kashi 75% na kuri’un kasar Ibo, 1,693,485. A yankinsa na Arewa maso gabas kuwa, ya iya samun 27% (1,255,357) ne.

Wasu su na ganin tsohon gwamnan na jihar Anambra ya taimakawa takarar Atiku a lokacin. Wannan karo sai yake takarar shugaban Najeriya.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Obi ya yarda ya sake karban tayin mataimakin shugaban kasa, ganin an ki warewa ‘Yan kudu tikitin na PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Peter Obi ya hakura da PDP
Peter Obi a lokacin yana PDP Hoto: @PeterObiGregory
Asali: Facebook

Gwamnoni sun yi bukulu

Amma sai gwamnonin kasar kudu maso gabas suka nuna za su ba Atiku goyon bayansu a zaben tsaida gwanin PDP ne idan ya dauke su, ya ajiye Obi.

Ganin cewa Obi ba zai tsira da ko kujerar mataimakin shugaban kasa ba, dole ta sa ya janye neman tikiti, ya kuma fice daga jam’iyyar tun da wuri.

Kara karanta wannan

2023: Dasuki ya samu takarar Majalisa a PDP, yana goyon bayan Tambuwal a kan Atiku

Wike ya caccaki Obi

Gwamnonin PDP masu karfi a yankin su ne: Ifeanyi Okowa, Godwin Obaseki, Ifeanyi Ugwuanyi, Okezie Ikpeazu, Udom Emmanuel da Nyesome Wike.

Da aka yi hira da shi, an rahoto Nyesom Wike yana cewa Peter Obi ba zai lashe zaben zama ‘dan takarar shugaban kasa ba ko da ya yi zamansa a PDP.

Da yake magana a ranar Alhamis, Premium Times ta ce gwamnan na Ribas ya ce bai yi mamakin matakin da tsohon gwamnan na Anambra ya dauka ba.

Wike ya ce tun da Obi ya sauka daga kujerar gwamnan Anambra a APGA, bai sake cin zabe a jihar ba, ya soki yunkurinsa na neman mataimaki a NNPP.

Babu maganar shiga NNPP

A jiya Doyin Okupe ya magantu bayan Peter Obi ya bada sanarwar ficewarsa daga PDP. Dr. Okupe shi ne Darekta Janar na jirgin yakin neman zaben Peter Obi.

Hadimin tsofaffin shugaban na Najeriya ya tabbatar da Obi ba zai nemi takara a jam’iyyar NNPP ba, ya ce Obi bai neman zama mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng