2023: Dasuki ya samu takarar Majalisa a PDP, yana goyon bayan Tambuwal a kan Atiku

2023: Dasuki ya samu takarar Majalisa a PDP, yana goyon bayan Tambuwal a kan Atiku

  • Abdussamad Dasuki ne zai yi wa jam’iyyar PDP takarar majalisa a yankin Kebbe da Tambuwal a 2023
  • Hon. Abdussamad Dasuki ya lashe zaben tsaida gwanin da aka shirya, ya lashe duka kuri’un PDP
  • Tsohon Kwamishinan ya bada shawarar a tsaida Aminu Tambuwal ya yi takarar shugaban kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Hon. Abdussamad Dasuki shi ne wanda ya yi nasarar zama ‘dan takarar PDP na yankin Kebbe da Tambuwal a majalisar tarayya a zaben 2023.

This Day ta ce tsohon kwamishinan kudin ya samu babbar nasara a zaben tsaida gwanin da jam’iyyar PDP ta shirya a ranar 22 ga watan Mayu, 2022.

Abdussamad Dasuki ya lashe duka kuri’u 65 da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP suka kada a zaben tsaida gwanin da aka gudanar kamar yadda sakamako ya nuna.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya sha kashi a zaben ‘dan takarar Gwamnan Kaduna, ya tsira da kuri’u 2

Da yake jawabi a gaban ‘yan jarida a ranar Litinin, Dasuki ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP masu kada kuri’ar zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa.

Tsohon kwamishinan harkar kudin na jihar Sokoto ya roki tawagar ‘yan PDP daga jihar da su zabi Mai gidansa watau Mai girma Aminu Waziri Tambuwal.

Atiku bai da farin jini

Har ila yau Dasuki ya maida martani a kan zancen da Dino Melaye ya yi kwanakin baya, yana cewa Atiku Abubakar yana da kuri’a akalla miliyan 11 a kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abdussamad Dasuki
Abdussamad Dasuki yana so ya koma Majalisa a PDP Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne ganin mutane miliyan 11 suka kada masa kuri’a a zaben 2019.

A cewar Dasuki, kuri’ar da Atiku Abubakar ya samu a zaben da ya wuce, shi ne mafi karancin da ‘dan takarar PDP ya taba samu a zaben shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

LP, NNPP, Jam’iyyu 4 da Peter Obi zai iya komawa kafin zaben 2023 bayan watsi da PDP

“Misali a 1999, Obasanjo ya doke Falae da kuri’a miliyan 18, Obasanjo ya doke Buhari da kuri’a miliyan 12, Yar’adua ya doke Buhari da kuri’a miliyan 24.”
“Jonathan ya doke Buhari da kuri’a miliyan. Haka zalika idan aka kamanta da 2015, Jonathan ya samu kuri’a miliyan 15, a lokacin da PDP ba tayi kokari ba.”

- Hon. Abdussamad Dasuki

Tambuwal ya dace da PDP

Sun ta rahoto ‘dan takarar majalisar tarayyar yana bada shawarar ‘yan PDP su yi watsi da Atiku Abubakar, a tsaida Rt. Hon. Aminu Tambuwal a PDP a zaben 2023.

Dasuki ya ce Tambuwal ya nuna yana da duk abin da ake bukata wajen rike Najeriya musamman a lokacin da ake bukatar wanda zai iya hada kan al’ummar kasar.

Shehu Sani ya sha kasa

Dazu kun ji labari cewa burin Shehu Sani na zama sabon gwamnan jihar Kaduna a 2023 ba zai cika ba, a sakamakon rashin nasarar da ya yi a zaben tsaida gwani.

‘Dan siyasar ya tabbatar da shan kashin da ya yi a shafin Twitter. Shehu Sani ya taya wanda ya samu nasara murna, ya yabawa mutane biyu rak da suka zabe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel