Da Duminsa: Dr. Dikko Radda ya lashe zaben fidda gwanin APC a jihar Katsina
- Tsohon darakta Janar na SMEDAN, Dr Dikko Umaru Radda, ya zama ɗan takarar gwamnan Katsina karkashin APC
- Radda ya samu tikitin APC ne bayan zama zakara a zaɓen fid da gwanin da ya gudana ranar Alhamis da kuri'u 506
- Yan takara Tara ne suka fafata a zaɓen kuma sun kunshi tsofaffin jami'an gwamnati da kuma yan kasuwa
Katsina - Dakta Dikko Umaru Radda, ya lashe zaben fitar da ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2023 na jam'iyyar APC.
Channels tv ta ruwaito cewa Radɗa ya samu kuri'u 506, haka ya bashi damar lallasa abokin hamayyarsa da ke take masa baya, Mustapha Inuwa, wanda ya samu kuri'u 442.
Haka nan kuma sakamakon zaben wanda aka bayyana da safiyar nan ya nuna cewa Abbas Umar Masanawa ne ya zo na uku da kuri'u 436.
Sauran sakamakon ya nuna cewa Sanata Abubakar Yar'adua ya samu kuri'u 32, Faruk Lawal Jobe ya samu 72, Abdulkarim Dauda Daura, ya samu kuri'a Bakwai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai kuma Umar Abdullahi Tsauri Tata ya samu kuri'u Takwas, Mannir Yakubu, ya samu guda 64 da kuma Ahmad Ɗangiwa, wanda ya sami kuri'u 220.
Shugaban kwamitin zaɓen na jihar Katsina, Kaka Shehu, wanda ya sanar da sakamakon, yace daga cikin Deleget 1,805 da suka fito daga gundumomi 261 na jihar, an tantance 1,801, guda hudu ne suka lalace.
Lagit.ng Hausa ta tattaro cewa yan takara Tara ne suka fafata a zaɓen fidda gwanin kuma sun kunshi tsoffin jami'an gwamnati da yan kasuwa.
Buhari ya gana da gwamnoni
A wani labarin kuma Kafin tafiya Malabo, Buhari ya gana da gwamnonin APC kan wanda jam'iyya zata tsayar ya gaje shi a 2023
Shugaban ƙasa Buhari ya gana da gwamnoni kan batun da ya shafi zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da ke tafe.
Wasu bayanai sun nuna cewa shugaban bai bayyana wa kowa wanda yake so ba, ya umarci a gudanar da sahihin zaɓe.
Asali: Legit.ng