Da duminsa: An yi garkuwa da 'yar takarar APC ana tsaka da zaben fidda gwani
- 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da 'yar takarar kujerar majalisar jiha a Filato ana tsaka da zaben fidda gwani a jam'iyyar
- An gano cewa, Honarabul Na'anyil Magdalene ta fita ganawa da deliget ne a ranar Alhamis da asuba amma aka sace ta
- Sun fita tare da kaninta Georgina amma suka kasa gane gidan da za su je, ya sauka ya nemo gidan amma ya dawo ya tarar babu ita ba labarinta
Plateau - 'Yar takara a karkashin jam'iyyar APC da ke hararo yin wuf da tikitin mazabar Qua'an Pan ta kudu da ke jihar Filato a zaben 2023, Honarabul Na'anyil Magdalene, an yi garkuwa da ita.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ubah Gabriel, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace kwamishinan 'yan sanda ya tura runduna ta musamman domin ceto ta, Daily Trust ta ruwaito.
An sace Magdalene a ranar da ake yin zaben fidda gwani na jam'iyyarta.
Magdalene, wacce a halin yanzu ita kadai ce mace a jam'iyyar APC da ke neman kujerar, an sace ta ne yayin da ta ke hanyar samun ganawa da wakilan jam'iyya wanda suka shirya a garin Kwalla da ke karamar hukumar Qua'an Pan na jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wata majiya daga yankin ta ce, "Honarabul za ta gana da deliget a ranar Laraba amma sun bata karfe 5:30 na asuban Alhamis. Ta tafi tare da kaninta Georagas amma sai suka kasa gane gidan, kaninta ya sauko daga motar kuma ya shiga yankin domin dubawa.
"Ya bar ta a cikin motar, amma abunda ya fi bata mamaki shi ne bai ganta ba da ya dawo. Wayoyinta duka suna cikin motar amma bai ganta ba."
Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi
A wani labari na daban, mutane bakwai ne suka halaka yayin da wasu uku suka jigata a ranar Talata, 24 ga watan Mayu yayin wani farmaki da 'yan ta'adda suka kai kauyukan Tungar-Wakaso, Dargaje, Farnanawa, Tsilligidi, Tudun-Gandu da Nannarki a kananan hukumomin Gummi da Bukkuyum a jihar Zamfara.
Miyagun wadanda aka kintata yawansu ya kai 150, sun bayyana wurin karfe 6 na yammaci, HumAngle ta ruwaito.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Alhaji Maidawa mai shekaru 53 mazaunin Tungar-Wakaso, ya samu harbin bindiga a bayansa, kwauri da kafadarsa yayin farmakin.
Asali: Legit.ng