Da Dumi-Dumi: Gwamnan Legas ya lashe zaɓen fidda gwanin APC, zai nemi tazarce a 2023

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Legas ya lashe zaɓen fidda gwanin APC, zai nemi tazarce a 2023

  • Gwamna Babajide Sanwo-olu ya lashe zaɓen fid da gwanin APC, ya zama halastaccen ɗan takarar gwamna a zaben 2023
  • Gwamnan Legas ɗin ya gode wa Allah bisa damar da ya ba shi tare da kira ga sauran yan takara su zo su haɗa kai
  • A ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu 2022 jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan ta gudanar da zaɓen tsayar da yan takara a zaɓen gwamnoni na 2023

Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC, ya zama ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.

An bayyana gwamnan a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen fitar da ɗan takarar gwamnan Legas karkashin APC wanda ya gudana a Mobolaji Johnson Sport Arena, Onikan, jahar Legas.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaba Jonathan ya yi zazzafan magana kan zaben fidda gwanin APC da PDP

Yan takarar gwamnan Legas.
Da Dumi-Dumi: Gwamnan Legas ya lashe zaɓen fidda gwanin APC, zai nemi tazarce a 2023 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sakamakom zaɓen ya nuna gwamnan ya samu kuri'u 1,170 daga cikin kuri'u 1,182 da aka kaɗa yayin zaɓen na yau Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai sauran yan takarar da ke neman tikitin APC su yi korafin cewa an hana su shiga a fafata da su a zaɓen fitar da ɗan takara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zamu ɗira daga inda muka tsaya - Sanwo-olu

Da yake martani bayan samun nasara, gwamnan ya ce:

"Ina gode wa Allah da Deleget da kuma shugabannin APC bisa damar da suka ba ni karo na biyu domin cigaba da kyakkyawan aikin da muka fara a jihar mu."
'Da wannan nasara da muka samu a zaɓen fid da gwani, ina da yaƙinin cewa kan mu a haɗe yake wuri ɗaya kuma a shirye muke mu cigaba da sadaukarwa ga jihar mu mai albarka."

Kara karanta wannan

Bidiyon wani ɗan takara ya duka kan guiwa yana godewa gwamna bayan lashe zaɓen fidda gwanin PDP

"Ga sauran yan takara kuma ina taya su murnan fafatawa a wannan matakin na demokaraɗiyya kuma ina gayyatar ku mu haɗa kai wajen ciyar da jahar mu gaba."

A wani labarin kuma Mataimakin Tambuwal da wasu mutum huɗu sun janye daga takara, tsohon Minista ya fice daga PDP

A jawabin shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin PDP a Sokoto ya sanar da sunayen mutum biyar da suka janye daga takara.

Ya ce mataimakin gwamna Tambuwal, shugaban PDP na jiha da wasu mutum uku sun janye daga shiga zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel