Da Dumi-Dumi: Sanata Ekweremadu ya janye daga zaɓen fidda gwani na PDP, zai koma APC

Da Dumi-Dumi: Sanata Ekweremadu ya janye daga zaɓen fidda gwani na PDP, zai koma APC

  • Sanata Ike Ekweremadu, ya janye daga shiga a dama da shi a zaben fidda gwani na yan takarar gwamnan jihar Enugu a PDP
  • Wasu bayanai sun nuna cewa tsohon shugaban majalisar dattawan na shirin ficewa daga PDP kuma da yuwuwar APC zai nufa
  • Duk da babu cikakken dalilin ɗaukar wannan matakin amma ana ganin hakan ba zai rasa alaƙa da rashin jituwarsa da gwamna mai ci ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Enugu - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya janye daga zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP a Enugu.

Darakta Janar da ƙungiyar kamfen ɗinsa, Charles Asogwa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanata Ike Ekweremadu.
Da Dumi-Dumi: Sanata Ekweremadu ya janye daga zaɓen fida gwani na PDP, zai koma APC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanarwan ta ce:

"Muna farin cikin sanarwa masoya da magoya bayan mu da Najeriya baki ɗaya cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattawa kuma ɗan takarar gwamnan Enugu, Sanata Ike Ekweremadu, ba zai shiga zaɓen fidda gwanin PDP ba."

Kara karanta wannan

Ko anini ba zan ba da ba: Shehu Sani ya ce ba dashi ba biyan deliget a zaben fidda gwani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Laraban nan da muke ciki, 25 ga watan Mayu, 2022, jam'iyyar PDP ta tsara zata gudanar da zaben fitar da yan takararta na gwamna a zaɓen 2023 da ke tafe.

Duk da dai babu wani cikakken bayani kan dalilin janyewar tsohon Sanatan, amma ana ganin ba zai rasa nasaba da rashin jituwar da ta shiga tsakaninsa da gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ba.

Da yuwuwar zai fice daga PDP

Wasu rahotanni sun nuna cewa tsohon ɗan majalisar ya gana da shugabannin APGA kan yuwuwar sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Babu wani cikakken bayani kan abin da suka tattauna amma jaridar ta gano cewa babu wata matsaya da ɓangarorin biyu suka cimma wa.

Amma da safiyar ranar Talata, wasu alamu sun nuna cewa Mista Ekweremadu, ka iya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC kuma ya nemi tikitin takarar gwamnan Enugu.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna a PDP

A wannan rana ne aka hangi Ekweremadu a ofishin Kamfen ɗin shugaban APC reshen Abuja suna tattaunawa, hakan wata alama ce ta yuwuwar shiga jam'iyyar su haɗa karfi wajen kwace mulki daga PDP a Enugu.

A wani labarin kuma wani ɗan takara a PDP ya yanke jiki ya faɗi bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta ƙasa a jihar Delta, Philip Okwuada, ya sume bayan jin yadda ta kaya a zaɓen fidda gwani.

Bayanai sun nuna cewa ɗan siyasan ya samu tabbacin samun nasara kafin zaɓen amma Deleget suka yaudare shi ya sha ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262