Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

  • Daga karshe dai wani dan kasuwan da ake zargi da sukar gwamnatin Inuwa Yahaya ya samu 'yancin ci gaba da yawo a kasa
  • Wannan na zuwa ne bayan ba da belinsa a karo na biyu ta hanya mai sauki daga wata babbar kotun jihar Gombe
  • An zargi dan kasuwan da caccakar gwamnatin Gombe ta yanzu da kuma kalubalantar ayyukanta, lamarin da masana suka ce yana da 'yancin tofa albarkacin bakinsa

Gombe - Wata babbar kotun jihar Gombe ta bayar da belin Bala Sani mai shekaru 47, wani dan kasuwa mazaunin Abuja da aka tsare bayan caccakar gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Daily Trust ta ruwaito yadda aka kama Sani a rumfar POS dinsa da ke Abuja aka kawo shi Gombe inda aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Yadda dan kasuwa ya kubuta daga kamen gwamna Inuwa Yahaya
Daga karshe: Dan kasuwan da ya shiga tasku saboda sukar gwamnan APC a Facebook ya kubuta | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

An tattaro cewa ya sha sukar Gwamna Yahaya tare da rubuta koke-koke domin kalubalantar daya daga cikin manufofin gwamnatin, kamar yadda 21st Century Chronicles ta ruwaito.

Laifukan da ya aikata

An fara gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata kotun Majistare a ranar 5 ga watan Maris, inda aka karanto masa tuhume-tuhume guda biyu na laifukan karya da kuma tada hankali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai ya ki amsa laifinsa, kuma alkalin kotun mai shari’a Babayo Abba Usamatu ya tura shi gidan yari.

Daga baya kotun ta bayar da belinsa, amma tsauraran sharuddan da aka gindaya ya sa wanda ake zargin ya kasa samun ’yancinsa.

An umarce shi da ya kawo wadanda za su tsaya masa, manyan sakatarorin dindindin guda biyu a jihar ko kuma hakiman gundumomi biyu, lamarin da ya kai shi zaman gidan yari sama da watanni biyu.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

Bai gamsu da sharuddan belin ba, lauyansa Haruna Luka ya garzaya kotu inda ya nemi a sake duba yanayin belin.

A zaman kotun na farko a ranar 5 ga watan Mayu, alkalin kotun mai shari’a Abdulhamid Yakubu, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Mayu, domin yanke hukunci kan neman belin.

A ci gaba da zaman kotun a ranar Litinin, Mai shari’a Yakubu ya yi nazari kan yanayin belin da kotun Majistare ta yi a baya tare da bayar da belin wanda ake tuhuma tare da wasu sharudda masu sauki.

Alkalin kotun ya umarce shi da ya kawo wadanda za su tsaya masa, dan uwa na jini da wani fitaccen mutum daga karamar hukumarsa ta asali.

Gwamna a Arewa Ya Ce an Gano Ɗanyen Man Fetur Fiye Da Ganga Biliyan 6 Jiharsa

A wani labarin, gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce Kamfanin Man Fetur na NNPC ta hannun wata kamfani mai neman man fetur ya gano danyen man fetur fiye da ganga biliyan 6 a yankin Kolmani.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Maryam Abacha ta maka Gwamna El-Rufai a gaban kotu

Ya bada tabbacin cewa gwamntinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an fara hako man danyen man da aka gano a masarautar Pindiga ta Jihar Gombe, rahoton Nigerian Tribune.

Inuwa ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da aka shirya domin karrama alkalin alkalai na wucin gadi na jihar Gombe, Hon Justice Muazu Abdulkadir Pindiga da aka yi a Pindiga a karamar hukumar Akko a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.