Karin bayani: Maryam Abacha ta maka Gwamna El-Rufai a gaban kotu

Karin bayani: Maryam Abacha ta maka Gwamna El-Rufai a gaban kotu

  • Maryam Abacha, matar marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja ta maka gwamnatin jihar Kaduna a gaban kotu
  • Tana bukatar kotun da ta bi mata hakkinta kan gidansu da ke Unguwar Rimi GRA da gwamnatin ta kwace duk da kuwa suna da takardun mallakar gidan
  • Tana bukatar kotun da ta sa gwamnatin jihar Kaduna da ta biya su N100 miliyan kan yadda aka tozarta su tare da buga sunan marigayin mijinta a jarida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Matar tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soji, Janar Sani Abacha, Hajiya Maryam Abacha ta maka gwamnatin jihar Kaduna a gaban kotu kan kwace wata kadarar mijinta da gwamnatin tayi a Unguwar Rimi da ke birnin Kaduna.

A cikin masu karar tare da Maryam Abacha akwai babban 'dan marigayin, Alhaji Mohammed Sani Abacha, rahoton Vanguard ya bayyana.

Kara karanta wannan

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

Wata sabuwa: Maryam Abacha ta maka Gwamna El-Rufai a gaban kotu
Wata sabuwa: Maryam Abacha ta maka Gwamna El-Rufai a gaban kotu. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Baya ga gwamnatin jihar Kaduna, ta hada da antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kaduna duk a cikin wadanda ta ke karar.

A takardun sammacin da lauyan iyalan Abacha, Dr Reuben Atabo, SAN mai lamba No.KDH/KAD/509/2022 da ya shigar gaban babbar kotun jihar Kaduna mai lamba 4, an umarci wadanda ake kara da su bayyana a gaban kotun bayan kwanaki 21 da samun sammacin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

In har kuwa wadanda ake kara suka ki bayyana, za a yanke hukunci a gaban masu kara duk da wadanda ake karar basu bayyana ba.

An karba sammacin kuma an shaida samun shi a ranar 16 ga watan Mayun 2022.

Iyalan Abachan na bukatar kotun da ta yi watsi da kwace kadararu da aka yi da ke gida mai lamba 1, titin Degel, Uguwar Rimi GRA Kaduna mai girman 3,705Sqr meters wanda ke da shaidar mallaka daga gwamnatin jihar Kaduna mai lamba No NC 11458.

Kara karanta wannan

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

Har ila yau, iyalan na bukatar umarni daga kotun wanda zai kange su daga wadanda suke kara, cibiyoyinsu, hukumominsu, hadimansu da duk wani abu da ya dangancesu daga aiki kan notis din kwace kadarar wacce darakta janar na KADGIS ya bayar na kwace kadarar.

Wadanda ke kaa suna bukatar a biya su kudi har N100,000,000 na cin mutuncin da aka janyo wa iyalan kan yadda aka wallafa sunan marigayi Janar Sani Abacha a jarida ba tare da wani dalili ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel