Mun gano take-taken, Goodluck Jonathan ne 'Dan takarar Buhari a zaben 2023 inji Kungiyar APC
- The APC Watchdog ta na zargin akwai masu shirin dawo da Goodluck Ebele Jonathan kan mulki
- Kungiyar ta nuna ba za ta amince a gama wahala, sannan Jonathan ya sake zama shugaban kasa ba
- Wahab Adewale ya ce Dr. Jonathan shi ne ‘Dan takarar da Shugaba Muhammadu Buhari yake so a APC
Abuja - Wata kungiya da ke cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fito ta na cewa akwai yiwuwar a ba Goodluck Jonathan takara a zaben 2023.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa wannan kungiya ta The APC Watchdog ta fitar da jawabi na musamman a game da shirin dawo da Dr. Goodluck Jonathan.
Shugaban The APC Watchdog na kasa, Alhaji Wahab Adewale, ya fitar da jawabi a karshen makon da ya wuce a Abuja, yana mai Allah-wadai da wannan yunkuri.
A cewar Wahab Adewale, tsaida Jonathan a matsayin ‘dan takarar shugaban Najeriya a APC, ba zai taimaki kowa ba, musamman wadanda suka kafa jam’iyyar.
Jonathan ne 'Dan takarar Buhari?
A madadin The APC Watchdog, jaridar ta rahoto Adewale yana cewa tsohon shugaban kasar shi ne wanda Muhammadu Buhari yake so ya mikawa mulki a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wannan kungiya ta APC ba ta iya bada hujjar da za ta gaskata wannan zargi da ta ke yi ba.
“Mun fahimci kulle-kullen da wasu masu rike da madafon iko su ke yi a dawo da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan jam’iyyarmu.”
“Wannan yunkuri ne da wani gwamna yake kitsawa, mu na fadawa masu wannan aiki cewa ba adalci ba ne, kuma ba zai taimaki APC ba.”
“Su gujewa wannan saboda zaman lafiyan daukacin ‘ya ‘yan jam’iyyarmu.” – Wahab Adewale.
APC Watchdog ta na ganin takarar Jonathan ba za ta kawo komai face sai rashin jituwa, la’akari da tirka-tirkar da aka yi kafin APC ta iya kafa gwamnati a 2015.
A karshen jawabin na sa, Adewale, ya tuna da yadda jam’iyyar APC ta sha wahala dare da rana shekaru bakwai da suka wuce domin kifar da gwamnatin PDP.
Wasu ba takara su ke yi ba
Ku na da labari cewa Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya zargi wasu masu neman shugabancin Najeriya da cewa ba da gaske suka shiga takaran ba.
Gwamna Kayode Fayemi ya ce cikin mutum 23 da ke neman tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a karkashin APC, kusan biyar ne kawai su ka shirya da gaske.
Asali: Legit.ng