Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023
- Mai martaba Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya nuna goyon bayansa ga kudirin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo na son gaje Buhari
- Basaraken ya bayyana cewa suna goyon bayan Osinbajo sannan za su saka shi a addu'a domin rokon Allah ya sa ya zama shugaban kasa a 2023
- Sarkin ya kuma yaba ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce ya yiwa kasar kokari sosai duk da tarin kalubale
Yobe - Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya bayyana cewa masarautarsa za ta marawa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo baya tare da saka shi a addu’a don Allah ya daura shi kan kujerar shugabancin Najeriya a 2023.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa sarkin ya dauki wannan alkawarin ne yayin da ya tarbi mataimakin shugaban kasar, wanda ya kai ziyarar ban girma fadarsa da ke Damaturu, babbar birnin jihar Yobe a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu.
Osinbajo ya ziyarci Yobe don ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Basaraken ya ce ziyarar da mataimakin shugaban kasar ya kai fadar alamu ne da ke nuna yana mutunta sarautar gargajiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Abin da muke tsammani shi ne ci gaba; daurawa a kan abin da aka kafa kuma mun doshi hanyar hakan.
“Don godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari; idan ka kawo maganar tsaro gwamnan mu zai ba da shaida kan abin da ya faru a jihar nan; abun da ya wakana a wannan jihar; amma da Buhari ya hau mulki sai al’amura suka gyaru; abubuwa sun inganta.
“Mun samu zaman lafiya a wannan gwamnati; Shugaba Buhari ya yi wa wannan kasa kokari sosai; yana kokari sosai duk da kalubale; akwai bukatar mu jinjinawa jagorancinku sosai.
“Da izinin Allah za mu saka ka a addu’o’inmu sannan za mu mara maka baya a dukkan bangarori don ganin cewa ka yi nasara, kuma a karshe muna addu’a cewa Allah ya sa ka zama shugaban wannan kasa mai albarka.”
El-kanemi ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ce ya sadaukar da kansa wajen gudanar da mulkin jihar tare da kulla kyakkyawar alaka da masarautar gargajiya, rahoton Vanguard.
Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari
A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, ya bayyana cewa yana da dukkan abun bukata domin gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Lawan ya bayyana hakan ne a garin Minna, babbar birnin jihar Neja, yayin da yake jawabi ga deleget din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihar, jaridar The Nation ta rahoto.
Mai neman takarar shugabancin kasar da tawagar kamfen dinsa sun gana da Gwamna Abubakar Sani Bello da deleget na zaben fidda dan takarar shugaban kasa sannan daga bisani suka kai ziyarar ban girma ga Sarkin Minna, Dr. Umar Farouq Bahago.
Asali: Legit.ng