Babbar magana: Gwamnan PDP ya rusa majalisar zartarwar jiharsa, ya kori mukarrabansa
- Rahoton da muke samu daga jihar Ribas ya bayyana cewa, gwmanan jihar ya rusa majalisar zartarsa
- Wannan na zuwa ne a yau Talata, amma dai gwamnan bai bayyana dalilin sauke manyan ma'aikatan ba
- Hakazalika, gwamnan ya sallami shugaban ma'aikata da daya daga cikin mataimakansa na musamman
Jihar Ribas - Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya rusa majalisar zartaswar jiharsa ba tare da bata lokaci ba, inji wani rahoton da muke samu daga jaridar The Nation.
Gwamnan, a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar, ya kuma sauke shugaban ma’aikatan fadarsa da kuma babban mataimakinsa (Protocol) daga mukamansu.
Punch ta ce sanarwar na cewa:
“Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya rusa majalisar zartarwa ta jihar daga ranar Talata, 24 ga Mayu, 2022.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Shugaban ma’aikata na gwamna da babban mataimaki na musamman (Protocol), suma an sauke su daga ofisoshinsu.
“Mai girma Gwamna Nyesom Ezenwo Wike, ya yabawa ‘yan majalisar zartarwa ta jihar Ribas bisa hidima da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar. Ya kuma yi musu fatan alheri a dukkan ayyukan da za su yi a nan gaba.”
Wike ya umurci daukacin tsoffin ‘yan mambobin majalisar zartarwar da su mika komai ga manyan jami’ai a ma’aikatun su.
Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo
A wani labarin na daban, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.
Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.
Asali: Legit.ng