Sanatan PDP ya fice daga filin zabe a fusace bayan ya sha kasa a wajen tsaida takara

Sanatan PDP ya fice daga filin zabe a fusace bayan ya sha kasa a wajen tsaida takara

  • Bangarorin Godwin Obaseki da na Dan Orbih sun gudanar da zaben tsaida gwaninsu a jihar Edo
  • A zaben da su Obaseki suka shiya, Mathew Iduoriyekemwen ne ya doke Sanata Mathew Urhoghide
  • Ganin ya rasa takarar 2023 a jam’iyyar PDP, Mathew Urhoghide ya bar wurin zabe ransa a fusace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Edo - Sanata Matthew Urhoghide mai wakiltar mazabar kudancin Edo a majalisar dattawa ya gagara samun tikitin jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Business Day a rahoton da ta fitar a yau, 24 ga watan Mayu 2022, ta bayyana cewa Hon. Mathew Iduoriyekemwen ne ya doke Matthew Urhoghide.

Rikicin cikin gidan jam’iyyar PDP a dalilin sabanin Gwamna Godwin Obaseki da jigon jam’iyya, Dan Orbih ya fito fili a zaben da aka yi a jihar Edo.

Kowane bangare ya gudanar da zaben fitar da gwaninsa da sunan shi ne ke rike da jam’iyya a Edo.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

A zaben da mutanen Obaseki suka shirya, tsohon ‘dan majalisar dokokin jiha, Hon. Mathew Iduoriyekemwen ne ya samu galaba da kuri’a 113.

Shi kuma Urhogide wanda yanzu haka yake rike da wannan mukami na Sanatan Kudancin Edo ya samu kuri’a 103, an ba shi ratar kuri’a 10 a zaben.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanatan PDP
Sanatan Edo ta Kudu Hoto: Senator Matthew Urhoghide
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce wannan lamari ya fusata Sanata Urhogide, har ta kai ya ki kula manema labarai.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Sanatan na jam’iyyar PDP ya fice daga wurin zaben ne ransa duk a bace, bai bari ‘yan jarida sun yi hira da shi ba.

Watakila Ordia zai zarce

A gefe guda kuma, Sanata Clifford Ordia ya sake zama ‘dan takarar Sanata na jam’iyyar PDP a mazabar jihar Edo ta tsakiya a babban zabe na 2023.

Haka zalika Victoria Edelokun ta samu tikitin PDP na Arewacin jihar ta Edo. Sanata Ordia da Edelokun sun samu nasara ne ba tare da hamayya ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sanatan PDP ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar

A bangaren Dan Orbih kuwa, ‘yan takarar na PDP su ne; Hon. Ogbeide-Ihama, Mike Onolememe da Pascal Ugbomeh, da alama lamarin zai kare a kotu.

Zaben tsaida gwani

An ji cewa Ibrahim Hassan Dankwambo ya ci takarar Sanatan Arewacin Gombe. Abubakar Aliyu da Anthony Yaro sun samu tikitin Sanata a PDP a jihar.

Sannan PDP za ta tsaida Banky W a matsayin ‘dan takararta a mazabar Eti-Osa. A Kaduna kuwa, irinsu Samaila Sulaiman da Sadiq Ango sun samu tikiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel