Zaben 2023: Sanatan PDP ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar

Zaben 2023: Sanatan PDP ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar

  • Sanata mai wakiltan yankin Ondo ta tsakiya, Ayo Akinyelure, ya rasa kudirinsa na komawa majalisar dattawa a zaben 2023
  • Kamar yadda sakamako ya nuna, Akinyelure, wanda ya kasance sanata sau biyu, ya sha kaye a hannun Ifedayo Adedipe a zaben fidda dan takarar sanata na PDP da aka yi
  • Bekekhimi Idiarhi, shugaban kwamitin zaben ya sanar da cewa Adedipe ya samu kuri’u 82 yayin da Akinyelure ya samu 58

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Sanata mai wakiltan yan kin Ondo ta tsakiya, Ayo Akinyelure, ya sha kaye a kudirinsa na son komawa majalisar dattawa karkashin inuwar jam’iyyarsa ta PDP kamar yadda aka sanar a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu.

Akinyelure, wanda ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa kan da’a, gata da korafe-korafen jama’a, ya sha kaye ne a hannun abokin hamayyarsa, Ifedayo Adedipe, a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Yadda Obasanjo ya sa mutum 9 suka yi sanadiyyar zaman Umaru Yaradua Shugaban kasa

Zaben 2023: Sanatan PDP ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar
Zaben 2023: Sanatan PDP ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar Hoto: @ayo_akinyelure
Asali: Twitter

Yayin da yake sanar da sakamakon a Akure, shugaban kwamitin zaben, Bekekhimi Idiarhi, ya ce Adedipe ya samu kuri’u 82, Akinyelure ya samu kuri’u 58, yayin da Clement Faboyede ya samu kuri’u 57.

Idiarhi ya ce an soke kuri’u biyu daga cikin jimlar kuri’u 199 da aka kada, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami’an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) sun sanya idanu a zaben, wanda aka yi cikin lumana da tsauraran matakan tsaro.

Da yake zantawa da manema labarai, Adedipe ya yi godiya ga deleget da shugabancin am’iyyar kan tabbatar da zabe na gaskiya da amana da suka yi.

Ya bukaci sauran masu takara da su kalli nasararsa a matsayin nasararsu dukka, yana mai bayyana cewa akwai aiki ja a gabansu, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Ta karewa Tinubu: Majiya ta ce APC ta gama zaban wanda zai gaji Buhari a 2023

Akinyelure da ya sha kaye a zaben fidda gwanin ya kasance sanata sau biyu.

Wani babban jigon APC a jihar Zamfara ya koma jam'iyyar PDP, ya shiga tseren takara a 2023

A wani labarin, wani jigon APC a jihar Zamfara, Ɗakta Dauda Lawal, ya fice daga jam'iyya mai mulki ya koma PDP, kamar yadda Chennels tv ta ruwaito.

Lawal, tsohon babban daraktan First Bank, ya kuma ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Zamfara ƙarƙashin inuwar sabuwar jam'iyyarsa PDP.

Ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi gaban dandazon masoya da magoya bayansa a gidansa da ke Gusau, babban birnin Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng