An shiga rudani, wasu sun 'sace' masu kada kuri’a wajen zaben tsaida ‘Yan takaran PDP

An shiga rudani, wasu sun 'sace' masu kada kuri’a wajen zaben tsaida ‘Yan takaran PDP

  • Kokarin fitar da ‘yan takarar jam’iyyar PDP a zaben ‘dan majalisa ya tada kura a wasu jihohi jiya
  • Rikici ya kaure tsakanin magoya bayan wasu ‘yan takaran PDP a karamar hukumar Gbako a Neja
  • A jihar Ogun, ana rade-radin an dauke wadanda za su zabi ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nigeria - Zaben tsaida ‘dan takarar da ake gudanarwa a jam’iyyar hamayya ta PDP ya cika da tarin rigingimu da hayaniya a wasu daga jihohi na kasar nan.

A wani rahoto da ya fito daga Daily Trust, an ji cewa wasu sun samu rauni wajen zaben fitar da gwanin da ake kokarin yi a Lemu, garin Gbako, jihar Neja.

Ba a iya karasa zaben fitar da gwani a kauyen Lemu ba a dalilin rikici da aka samu tsakanin magoya bayan Alhaji Gimba Tswatagi da na Nma Busokun.

Kara karanta wannan

Mai neman takara ya samu tikitin PDP yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane

Rahoton da mu ka samu ya ce an tsaida zaben bayan magoya bayan ‘yan takarar sun aukawa junansu da makamai, a karshe dai malamin zabe ya tsere.

Abin farin cikin shi ne PDP ta gudanar da zabe lafiya kalau a wasu garuruwan na Neja irinsu Lavun, Edati, Mokwa, Shiroro, Chanchaga, Bosso, da Gurara.

Rudani a Ogun

A jihar Ogun, jaridar ta ce ana zargin an yi garkuwa da wadanda ke kada kuri’a domin fito da ‘dan takara. Wannan ya jawo rudani da bata lokaci wajen yin zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan takaran PDP
Magoya bayan PDP a taro siyasa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ba a iya gudanar da zaben tsaida gwanin ‘dan takarar majalisar tarayya a yankin Abeokuta ta Arewa/ Odeda/Obafemi-Owodeda da Abeokuta ta Kudu I da II ba.

Har zuwa bayan karfe 6:00 na yammacin ranar Lahadi, ba a cin ma matsaya tsakanin ‘ya ‘yan PDP a kan yadda za a fito da ‘yan takara a duka mazabun Abeokuta ba.

Kara karanta wannan

Bayan fille kan ‘Dan Majalisa da sace wani dan siyasa, ‘Yan bindiga sun ce 'za su dawo'

Malamin zaben da PDP ta tura, Abimbola Ademuyiwa tabbatar da cewa an samu sabani wajen zaben, hakan ya jawo wankin hula ya kai wa jam'iyyar PDP dare.

Sai bayan karfe 8:00 aka fara shirin kada kuri’ar tsaida ‘yan takarar ‘dan majalisa. Rotimi George Taylor mai neman tikiti ya tabbatar da zargin satar masu yin zabe.

Taylor ya shaidawa 'yan jarida an yi garkuwa da wasu daga cikin masu kada kuri’a a zaben da nufin a tursasa su wajen tsaida ‘dan takarar majalisa da karfin tsiya.

Amma Sakataren PDP na Ogun, Sunday Solarin ya musanya zargin sace masu kada kuri’a. Mista Solarin ya ce an canza wurin yin zaben ne saboda matsalar tsaro.

The Nation ta ce haka abin ya faru a yankunan Akwa Ibom Bayelsa da Ondo da jihar Delta. A Edo kan 'Yan PDP ya rabu biyu, yayin da aka daga zabukan Imo da Filato.

Kara karanta wannan

Tambuwal da Gwamnoni 9 masu neman mulki su na kashe miliyoyi duk rana a hayar jirgi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng