Buhari Ya Taka Rawar Gani Ko Mutane Suna So, Ko Ba Su So, In Ji Gwamnan APC

Buhari Ya Taka Rawar Gani Ko Mutane Suna So, Ko Ba Su So, In Ji Gwamnan APC

  • Dave Umahi, gwamnan Jihar Ebonyi ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tabuka abin azo a gani a mulkinsa ko ana so, ko ba a so
  • Dan takarar shugaban kasar na APC a zaben 2023 ya furta hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa na Politics Today a Channels Television
  • Umahi ya ce idan an zabe shi shugaban kasa zai dora daga inda Buhari ya tsaya yana mai cewa zai maimaita abin da ya yi a jiharsa a matakin kasa

Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Lahadi ya jinjina wa kokarin da gwamnati mai ci yanzu kan tafiyar da al'amurran kasar, rahoton Channels Television.

Umahi, daya cikin yan takarar shugaban kasa a APC ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya taka rawar gani wurin jagorancin kasar tun da ya kama ofis a 2015.

Kara karanta wannan

Lalong: Abin Da Yasa Ba Zan Goyi Bayan Ɗan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewa Ba a APC

Buhari Ya Taka Rawar Gani Ko Mutane Suna So, Ko Ba Su So, In Ji Gwamnan APC
Buhari Ya Taka Rawar Gani Ko Mutane Suna So, Ko Ba Su So, In Ji Umahi. Hoto: The Punch.
Asali: Facebook

Zan dora daga inda Buhari ya tsaya idan an zabe shi shugaban kasa, Umahi

"Idan ana maganan alkalluma ne na cigaba da za a dora a kai, tabbas Shugaban kasa ta taka rawar gani, ko kana so, ko ba ka so. Idan ayyuka ne, tsaro, tattalin arziki, hada kan yan Najeriya, ina tunanin Allah ya taimake shi ya taka rawar gani a kowanne cikinsu," a cewarsa yayin hirar da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na Channels Television.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yan Najeriya sun gaji da alkawurra na yan siyasa. Suna son ganin hujjar aikin da ka yi ne. Ina da hujjan ayyukan da na yi kuma na yi imanin zan maimaita hakan a matakin kasa."

Ya cigaba da magana kan yadda gwamnati mai ci yanzu ta tafiyar da batun tsaro yana mai cewa ta yi kokari sosai.

Kara karanta wannan

Ana Zaman Ɗar-Ɗar Yayin Da Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai

Umahi ya yi imanin cewa kallubalen tsaron da zai fi haka muni idan da ba Buhari bane ke mulki, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mara riko a zuci.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164