Da duminsa: Tinubu ya dira jihar Yobe domin janyo hankalin wakilan jam'iyya

Da duminsa: Tinubu ya dira jihar Yobe domin janyo hankalin wakilan jam'iyya

  • Jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi dirar mikiya a garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe
  • Dan takarar shugaban kasan karkashin jam'iyyar APC ya isa garin ne domin samun ganawa da wakilan jam'iyyar na jihar
  • Mataimakin gwamnan jihar ne ya karbe shi bayan isarsa, kuma zai zarce wurin gwamna daga nan ya wuce kai gaisuwa ban girma ga Sarkin Damaturu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe - Babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dira jihar Yobe domin zantawa da wakilan jam'iyyar APC yayin da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa ke gabatowa.

Jihar Yobe jiha ce ta jam'iyyar APC kuma gida ne ga tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni, jaridar The Nation ta ruwaito.

Da duminsa: Tinubu ya dira jihar Yobe domin janyo hankalin wakilan jam'iyya
Da duminsa: Tinubu ya dira jihar Yobe domin janyo hankalin wakilan jam'iyya. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Tinubu ya isa jihar Yobe ne ta jirgin sama inda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Damaturu kuma aka karbe shi hannu bibbiyu.

Kara karanta wannan

Ka zabi Ganduje matsayin mataimakin shugaban kasa, an yi kira ga Tinubu

Mataimakin gwamna Idi Barde Gubana, Wazirin Fune shi ne ya jagoranci shugabannin jam'iyya, 'yan majalisar jihar, kwamishinoni, masu bada shawara na musamman da manyan masu ruwa da tsakin APC wurin tarar Tinubu a filin jiragen sama da ke Kallalawan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana tsammanin jigon APC zai kai ziyara ga Gwamna Buni tare da mika gaisuwar ban girma ga Sarkin Damaturu, Alhaji Shehu Hashimi 11 ibn Umar el Amin Elkanemi kuma dagabisani ya gana da wakilan jam'iyyar a dakin taro na Banquet da ke gidan gwamnati a Damaturu.

Gwamna Ganduje da jiga-jigan APC su tarbi Bola Tinubu a Filin Aminu Kano

A wani taro na daban, jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, yanzu haka yana Kano a wani sashin yawon neman shawari game da burinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya nada sabon Shugaban hukumar lissafi da kididdiga

Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jiga-jigai, mambobi da Deleget na jam'iyyar APC yayin da ya dira a filin jirgin Malam Aminu Kano, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shi ne ya jagoranci tawagar shugabannin jam'iyya zuwa wurin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasa.

Baki ɗaya mutanen da suka je wurin taryan ciki har da gwamna Ganduje sun sanya kaya iri ɗaya da hula masu ɗauke da alamar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel