Da duminsa: Buhari ya nada sabon Shugaban hukumar lissafi da kididdiga

Da duminsa: Buhari ya nada sabon Shugaban hukumar lissafi da kididdiga

  • Shugaba Buhari ya nada sabon shugabar hukumar bincike, lissafi da kididdiga ta Najeriya
  • Hukumar ta NBS ke da hakkin bincike da kiddigar hauhawa da saukar tattalin arzikin Najeriya
  • Shugaban kasan yanzu haka ya tafi hadaddiyar daular larabawa don kai gaisuwar ta'aziyya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mr Semiu Adeyemi Adeniran matsayin sabon Shugaban hukumar lissafi da kididdiga na Najeriya (NBS).

Nadin Mr Semiu ya biyo bayan mutuwar tsohon shugaban hukumar, Dr Simon Harry, wanda ya mutu ranar 13 ga Afrilu, 2022.

Sufuyan Ojeifo, mai magana da yawun karamin ministan kudi, Prince Clem Agba, ya bayyana cewa sabon shugaban hukumar mutum ne wanda ya kware wajen harkar lissafi.

Yace:
"Tsawon shekaru 30 ya samu kwarewa wajen aikin daga makarantun gida da na waje."

Kara karanta wannan

Bayan Kwana Uku a Tsare, EFCC Ta Sako Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Gabanin nadinsa, ya kasance Diraktan binciken yanki-yanki na hukumar kididdiga ta tarayya."
Semiu
Da duminsa: Buhari ya nada sabon Shugaban hukumar lissafi da kididdiga
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya nada Dr Tutuwa Adamu matsayin shugabar FIIRO

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Dr. Adamu Tutuwa matsayin Dirakta Janar na hukumar binciken masana'antun tarayya watau Federal Institute of Industrial Research, Oshodi FIIRO.

Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar Kimiya da Fasaha, Mrs. Monilola Udoh, ce ta fitar da sanarwar ranar Juma'a a jihar Legas.

A cewar sanarwar, Dr Adamu Tutuwa ta kasance Diraktar hukumar hukumar cigabar fasahar ilmin hallita na tarayya watau National Biotechnology Development Agency, shiyyar Jalingo, jihar Taraba gabanin sabon nadin da aka yi mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel