Lalong: Abin Da Yasa Ba Zan Goyi Bayan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ba a APC
- Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce ya na goyon bayan tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi akan takarar shugaban kasar da ya ke yi
- Ya ce ba zai taba goyon bayan wani dan arewa ba saboda Amaechi ya yi wa jiharsa kokari sosai kuma yanzu ne lokacin da ya fi dacewa su saka masa
- A cewarsa, ya na da duk halayen kirkin da shugaba ya dace ya mallaka kuma shi ne kadai zai iya kawo ci gaba a duk bangarorin kasar nan
Filato - Simon Lalong, ya ce yana goyon bayan Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri kuma dan takarar shugaban kasa na 2023, ya kuma ce ba zai bi bayan wani dan takara daga arewacin Najeriya ba.
The Punch ta ruwaito ta rahoto cewa Lalong ya yi wannan ikirarin ne a Jos, lokacin da Amaechi ya je jihar don jan hankalin wakilan jam’iyyarsu yayin da zaben fidda gwani ya ke kunno kai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Lalong, Amaechi ya taka babbar rawa a jiharsa don haka zai samu goyon baya daga duk shugabannin Filato, ciki har da tsohon kakakin majalisar tarayya da ‘yan majalisar jihar.
Ya ce Amaechi ne kadai zai iya kawo karshen rashin tsaro
A wata takarda wacce ya bai wa manema labarai a ranar Asabar, an yanko inda Lalong ya ke cewa:
“Amaechi ya na da duk halayen shugaba na kwarai kuma shi ne zai ceto kasar nan daga matsalar rashin tsaro sannan ya ciyar da sauran bangarorin kasar nan gaba inda ya ce Jihar Filato ta amfana da Amaechi don haka yanzu ne lokacin biyansa.”
The Punch ta nuna yadda Lalong ya tsaya akan cewa Amaechi ya na da ikon ganin bayan rashin tsaron Najeriya, kuma kwararre ne a harkar tsaro da dabaru.
Ya yi kira ga jiga-jigan jam’iyyar APC na arewa musamman na Jihar Filato da su yi rijista da jam’iyyar. Ya kuma ce tsohon ministan ya dade ya na yin magana a maimakon jihar a duk wasu taro na majalisar tarayya idan bukatar hakan ta tashi kuma da gaggawa fadar shugaban kasa ta ke amsar bukatunsu.
“Ka yi kokari kwarai a Jihar Filato shiyasa za ka girbi abinda ka shuka. Amaechi ministanmu ne, bai damu da cewa daga Jihar Ribas ya ke ba. Muna samun kusan komai,” in ji Lalong.
‘Yan majalisar jihar su na goyon bayan Amaechi
Ya kara da tuna yadda Amaechi ya tura wasu daga jiharsa zuwa kasar China wadanda yanzu haka sun kusa zama kwararru a fannin aikin injiniya, banda sauran abubuwa na arziki da ya yi wa jihar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Jihar Filato, Yakubu Sande ya nuna goyon bayansa ga Amaechi inda ya ce:
“Yanzu haka duk mambobin majalisar jihar Filato, shugabannin kananun hukumomi 17 da jihar ke da su, wakilan jam’iyyar na tarayya da jiha za su mara masa baya.”
Asali: Legit.ng