Zaben 2023: Babban abin da ya sa har gobe Shugaba Buhari yake kaunar Amaechi - El-Rufai
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya maidawa Nasir El-Rufai martani a kan wata maganar da ya yi
- Gwamna Nasir El-Rufai ya ce sun rika yin zama da ‘Yan G-7 da suke shirin komawa APC a 2014
- Sule Lamido bai da labarin haduwa da El-Rufai ko tunanin ficewa daga PDP zuwa jam’iyyar APC
Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yi karya da ya fadawa Rotimi Amaechi cewa shi da wasu sun yi shirin barin PDP.
Jaridar nan ta Premium Times ta kawo wannan rahoto a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022.
Sule Lamido ya ce maganar da Gwamnan Kaduna ya yi na cewa shi da wasu gwamnonin PDP shida sun yi niyyar dawowa jam’iyyar APC, ba gaskiya ba ne.
Da yake bayani yayin da Rotimi Amaechi ya ziyarci jihar Kaduna domin samun goyon bayan ‘yan jam’iyyar APC, Nasir El-Rufai ya bijiro da wannan maganar.
El-Rufai ya kawo labarin yadda ya hadu da Amaechi a tarihi, ya ce sun yi kicibis a siyasa ne lokacin da Gwamnonin G7 suka nemi su sauya-sheka a 2014.
“Lokacin da mu ka fara tattaunawa da G-7, Gwamnoni bakwai da suka so su shigo APC. Ina zama da Amaechi da Gwamnan Adamawa, Nyako.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Daga baya sai mu ka samu biyar daga cikinsu da suka shigo jam’iyyarmu, daga nan lissafi ya canza.” - Nasir El-Rufai.
Amaechi ya saida rayuwarsa a 2015
A cewar El-Rufai, Amaechi ya yi kasada a lokacin yana Gwamnan Ribas, ya fice daga PDP yayin da Goodluck Jonathan yake kan kujerar shugaban Nejeriya.
Wannan kasada da Amaechi ya yi shiyasa shugaba Buhari yake kaunarsa har gobe inji gwamnan.
Jaridar ta ce har wa yau, gwamnan na Kaduna ya bada labarin yadda Amaechi ya taimaka masu da kudin yin gangamin siyasa a sa’ilin da suke jam’iyyar CPC.
Wannan ba gaskiya ba ne - Sule Lamido
Amma Sule Lamido yace ba haka abin yake ba, bai taba sanin gwamnonin G-7 sun hadu da El-Rufai ba, har su yi maganar sauya-sheka zuwa APC a lokacin.
“Babu lokacin da mu ka zauna, mu ka yanke hukuncin komawa APC, da har za a ce wasu gwamnoni sun ji tsoro, dole in bayyana gaskiyar lamarin.”
- Sule Lamido
Tsohon gwamnan na Jigawa ya ce maganar El-Rufai ta nuna da dukiyar Ribas aka kafa APC, sannan ya ce sa'ilin nan ba su san Amaechi ya na tare da APC ba.
Asali: Legit.ng