Gwamna Ganduje da jiga-jigan APC su tarbi Bola Tinubu a Filin Aminu Kano
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya jagoranci jiga-jigan APC da masoya wajen tarban Bola Tinubu a Aminu Kano
- Duk da matsanancin ruwan da aka zabga a Kano, hakan bai hana taruwar magoya baya ba a kofar shiga filin jirgin
- Jagoran APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ya dira Kano ne domin ganawa da masu ruwa da tsaki da Deleget
Kano- Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, yanzu haka yana Kano a wani sashin yawon neman shawari game da burinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023.
Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jiga-jigai, mambobi da Deleget na jam'iyyar APC yayin da ya dira a filin jirgin Malam Aminu Kano, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shi ne ya jagoranci tawagar shugabannin jam'iyya zuwa wurin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasa.
Baki ɗaya mutanen da suka je wurin taryan ciki har da gwamna Ganduje sun sanya kaya iri ɗaya da hula masu ɗauke da alamar Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da matsanancin ruwan sama da ake yi a lokacin amma kofar shiga filin jirgin cike take da ɗumbin masoya dake jiran fitowar wanda suka je dominsa.
Ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda aka yi tsammanin isarsa da misalin ƙarfe 11:00na safe, jirginsa bai dira a Kano ba sai da yamma misalin ƙarfe 5:00 saboda tsananin ruwan sama.
Tinubu ya kama Kano
Ana ganin jihar Kano babbar ginshiƙi ce ga Tinubu domin ko da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ziyarci jihar Ranar Laraba, ya faɗi inda soyayyar gwamna ta nufa.
Tsohon gwamnan Ribas ɗin yayin ganawarsa da Deleget, ya gaya wa gwamna Ganduje cewa APC ta san inda akalar goyon bayansa ta nufa.
A wani labarin kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje
Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.
Asali: Legit.ng