Hukumar EFCC ta gano gidajen Akanta Janar guda 17 a Landan, Abuja, Legas, Kano da Dubai

Hukumar EFCC ta gano gidajen Akanta Janar guda 17 a Landan, Abuja, Legas, Kano da Dubai

  • Bayanai sun fara bayyana kan dukiyoyin da Akanta Janar, Ahmed Idris ya mallaka a fadin duniya
  • An damke Akanta Janar din ne bisa zargin almundahanar makudan kudi da suka kai nairan bilyan tamanin
  • Hukumar hana almundahanan tace nan ba da dadewa ba zata gurfanar da shi gaban kuliya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta bankado gidajen Akanta Janar na tarayya, Ahmad Idrs, guda goma sha bakwai (17).

Punch ta ruwaito cewa wani jami'in EFCC wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace Idris ya mallaki gidaje a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London

Ya kara da cewa an gani Ahmad Idris ya yi amfani da wasu makusantarsa wajen sayen wadannan dukiyoyi.

Jami'n yace ga dukkan alamu, ya mallakai wadannan dukiyoyin ne yayinda yake Ofis amma bai ayyana cikin takardar hukumar ladabtar da ma'aikata ba kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Yace:

"Kimanin gidaje 17 a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London aka bankado mallakinsa. A Abuja, wasu gidajen na manyan rukunin gidaje."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta gano gidajen Akanta Janar guda 17 a Landan, Abuja, Legas, Kano da Dubai
Asali: Facebook

Ministar kudi ta dakatar da Akanta-Janar

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta dakatar da babban akanta-janar na tarayya, Ahmed Idris, har sai baba-ta-gani.

Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama shi kan zargin wawure kudi naira biliyan 80.

A wata wasika mai kwanan wata 18 ga watan Mayu, 2022, Ahmed ta ce dakatarwar ‘ba tare da biya ba’ ya kasance ne domin bayar da damar yin bincike a tsanaki ba tare da cikas ba daidai da dokokin aikin gwamnati.

Ba a bukatar ya zo ofis ko kuma ya tuntubi kowani jami’I a ofishinsa sai dai don wani zama na ladabtarwa wanda za a iya bayar da shawara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel