Jerin gwamnonin APC da na PDP da basa neman zarcewa a 2023
A kundin tsarin mulkin Najeriya, an ba gwamnoni damar yin shugabanci na tsawon wa’adi biyu ne kawai, wanda ya yi daidai da jimlar shekaru takwas.
Don haka, bayan kammala shekaru takwas a kan kujerar shugabanci, ba za su iya neman wa’adi na uku ba kamar yadda yake a doka.
Gabannin zaben 2023, akalla gwamnoni 17 daga jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) ne suka fada a wannan rukunin.
Gwamnonin PDP
1. Okezie Ikpeazu (Abia)
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Emmanuel Udom (Akwa Ibom)
3. Samuel Ortom (Benue)
4. Ifeanyi Okowa (Delta)
5, Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu)
6. Nyesom Wike (Rivers)
7. Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto)
8. Darius Ishaku (Taraba)
Gwamnonin APC
1. Ben Ayade (Cross River)
2. Dave Umahi (Ebonyi)
3. Mohammed Badaru Abubakar (Jigawa)
4. Nasir El-Rufai (Kaduna)
5. Abdullahi Umar Ganduje (Kano)
6. Aminu Bello Masari (Katsina)
7. Atiku Bagudu (Kebbi)
8. Abubakar Sani Bello (Niger)
9. Simon Lalong (Plateau)
Tunda ba za su iya sake takarar kujerar gwamna ba, wasu daga cikin gwamnonin da aka lissafa suna neman zama shugaban kasa ko sanatoci a zaben 2023.
Yawancinsu idan ba duka ba suna cikin siyasa don tabbatar da ganin yan siyasar da suka fi so sun gaje su a matsayin gwamnoni a 2023.
2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka
A wani labarin, wani dan takarar gwamna a jihar Plateau, Ambasada Yohana Margif, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Margif, wanda ya siya fom din takara na zaben gwamna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a cikin wata sanarwa da ya saki ga manema labarai a garin Jos, a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu, jaridar Punch ta rahoto.
Har ila yau, ya sanar da hukuncin da ya yanke a cikin wata wasika wanda aka gabatawar shugaban APC na gundumar Margif/Kopmur da ke Mushere, karamar hukumar Bokkos, wadda aka mika kwafinta ga shugabannin APC na karamar hukuma da na jaha.
Asali: Legit.ng