Jerin yan takarar shugaban ƙasa da suka sayi Fom N100m kuma suka canza shawara

Jerin yan takarar shugaban ƙasa da suka sayi Fom N100m kuma suka canza shawara

Jam'iyyar All Progressive Congress APC ta bayyana sunayen yan takarar shugaban ƙasa da suka sayi Fom miliyan N100 kuma suka gaza cikewa su mayar.

Idan masu bibiyan mu ba su manta ba jam'iyyar APC mai mulki ta saka N30m a matsayin kudin Fom ɗin nuna sha'awa da kuma miliyan N70m kuɗin Fom ɗin tsayawa takara.

Makudan kuɗin da jam'iyya mai mulki ta sanya wa Fom ɗin takarar shugaban ƙasa N100m ya jawo zazzafan raddi daga yan Najeriya.

Wasu mutane sun bayyana cewa jam'iyyar ta tsananta duba da yanayin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasar nan.

Yan takara uku ba su maida Fom ba.
Jerin yan takarar shugaban ƙasa da suka sayi Fom N100m kuma suka canza shawara Hoto: CBN, Aisha Buhari, Temipre Sylva
Asali: Facebook

Da yake jawabi a ranar Laraba 18 ga watan Mayu, 2020 a wata hira da kafar Channels tv wacce The Cable ta bibiya, Felix Morka, Sakataren tsare-tsare na APC ta ƙasa, ya ce mutum uku ba su dawo da Fom ɗinsu ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi, yace sun gama wahala a duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum ukun su ne kamar haka;

1. Ministan kwadugo da rage zaman kashe wando, Dakta Chris Ngige.

2. Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

3. Ƙaramin ministan albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Ngige da Sylva na cikin mambobin majalisar gwamnatin Buhari, waɗan da suka canza shawara bayan shugaban ƙasa ya umarci masu burin takara su yi murabus.

Mista Morka ya ce:

"Muna da yan takara 28 da gaba ɗayan su suka karɓi Fom, a ƙididdiga ta ƙarshe mun samu 25 sun maido da Fom ɗinsu."
"Uku daga cikin su basu dawo mana da Fom ba, sune; Sanata Chris Ngige, Godwin Emefiele da Timipre Sylva, duk ba su maido mana da Fom ba."

A wani labarin kuma An gano mutanen da suka taimaka wa yan bindiga suka kai sabon hari hanyar Abuja-Kaduna

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan bindiga sun banka wuta a Kamfanin rarraba wutar lantarki, sun tafka ɓarna

Jami'an tsaro sun dora alhakin kai sabon hari hanyar Kaduna-Abuja kan masu kwarmata wa yan bindiga bayanan sirri.

A cewar wani babban jami'i Imfomomi da ke zaune a kauyukan yankin ne suka jawo harin ta hanyar taimaka wa yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel