Tsohon ministan Buhari: Na fi Osinbajo da Tinubu cancantar gaje kujerar Buhari
- Ministan Buhari ya bayyana a jihar Kano, ya fadi irin abubuwan da ya taka na shirin gaje Buhari a zaben 2023 mai zuwa
- Amaechi ya ce shi ya fi cancanta ya dane kujerar Buhari a 2023 kasancewarsa mai gogewar da ta fi kowa
- Balo-balo, ya fito ya ce ya fi Tinubu da mataimakin shugaban kasa Osinbajo cancantar hawa kujerar shugabancin kasar nan
Jihar Kano - Tsohon Ministan Sufuri kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Rotimi Amaechi, a Kano ranar Laraba ya ce ya fi shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Ahmed Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo cancantar gaje Buhari.
Sai dai kuma gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi dabarar kaucewa nuna goyon baya ga Amaechi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Amaechi ya ziyarci Kano ne a ranar Laraba a wani bangare na neman shawari gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, rahoton Tribune Online.
Amaechi ya shaida wa Ganduje cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na san matsayarka game da batun takarar shugaban kasa na jam'iyyarmu, kuma ina so ka canza saboda ni."
Amaechi ya kara da cewa ya fi Tinubu cancanta, ganin cewa tsohon gwamnan na Legas bai taba zama minista ba, kuma ko a matsayinsa na Sanata, Tinubu ya shafe aikin watanni ne kawai, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.
Hakazalika ya bayyana cewa ya fi mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo cancanta, inda ya ce yayin da Osinbajo yake kwamishina a Legas, ya taba zama kakakin majalisar dokokin jihar Ribas.
Ganduje Da Barau Sun Bi Murtala Garo Har Gida Don Ƙoƙarin Hana Shi Ficewa Daga APC
A wani labarin, gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Jibrin sun ziyarci dan takarar mataimakin gwamna na sassanci a APC, Murtala Garo, bayan karfe 12 na daren Alhamis.
Daily Nigerian ta tattaro cewa gwamnan, a wata fita da ya yi ba tare da cikakken tawagarsa ba, ya ziyarci gidan Garo da ke Railway Quaters don rokonsa kada ya fita daga APC.
Wata majiya wacce ke da masaniya kan lamarin ta ce Ganduje ne ya fara isa gidan kafin daga bisani Jibrin ya iso ya tarar da shi.
Asali: Legit.ng