‘Dan takaran NNPP da ya bi Ganduje, ya janye jiki ya dawo Kwankwasiyya bayan awa 24

‘Dan takaran NNPP da ya bi Ganduje, ya janye jiki ya dawo Kwankwasiyya bayan awa 24

  • Yusuf Ibrahim Sharada ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC bayan ya rasa samun takara a NNPP
  • Sharada ya nemi ya tsaya a matsayin ‘dan majalisar Birnin Kano, sai NNPP ta tsaida Sagir Koki
  • Wasu su na korafi a kan yadda aka bi wajen zakulo wadanda za su yi wa jam’iyyar adawar takara
  • Kafin a je ko ina sai aka ji Sharada ya na bada sanarwar watsi da bin Ganduje da dawowarsa PDP

Kano - Siyasar Kano ta na cigaba da rikida tun da Rabiu Musa Kwankwaso ya bada sanarwar ficewarsa daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP a watan Maris.

A ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022, jam’iyyar NNPP ta zabi wadanda za su tsaya mata a matsayin ‘yan takara a jihar Kano a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Shekarau: Abin Da Ya Sa Na Fita Daga APC Na Koma NNPP Don Haɗuwa Da Kwankwaso

Legit.ng Hausa wannan zabi da aka yi ya bar baya da kura a siyasar Kano, inda wasu cikin ‘yan siyasan da suka saye fam su ke ganin ba ayi masu adalci ba.

Yusuf Ibrahim Sharada yana cikin wadanda aka fusata bayan an fitar da jerin ‘yan takara.

Kamar yadda mu ka ji labari, Malam Yusuf Ibrahim Sharada mai neman kujerar Birnin Kano a majalisar wakilan tarayya ya yi wuf, ya bar Kwankwasiyya.

Mai taimakawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a dandalin sada zumunta, Abubakar Aminu Ibrahim ya tabbatar da cewa Sharada ya shiga jam’iyyar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Dan Kwankwasiyya ya jefar da jar hula
Yusuf Ibrahim Sharada tare da Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: Abubakar Aminu Ibrahim @aaibrhim1
Asali: Facebook

Kafin ya fito daga ganawar da ya yi da gwamna, sai aka ga Sharada ya cire jar hularsa, ya maye gurbinta da baka. Jar hula alama ce ta mabiyar Kwankwasiyya.

Abubakar Aminu Ibrahim ya fitar da jawabi

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP ta fitar da duk wadanda za su yi mata takaran zaben 2023 a jihar Kano

“Hon. Yusuf Sharada mai neman wakiltar Birnin Kano a takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya ya sauya-sheka zuwa jma’iyyar APC.
Mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje OFR ya karbe shi a gidan gwamnatin jihar Kano a yau Alhamis, 19 ga watan Mayu 2022.”

- Abubakar Aminu Ibrahim

Sagir Koki ya samu takara

Malam Sharada yana cikin matasan da ake ji da su a tafiyar Kwankwasiyya. Tun tuni ya saye fam a jam’iyya mai kayan marmari, amma Sagir Koki za a ba tikiti.

Koki Injiniya ne wanda ya yi karatunsa a jami’ar Bayero da ke Kano shekaru kusan 30 da suka wuce. Bayan nan ya karanci ilmin kasuwanci a kasar Holland.

Shugaban kamfanin na Starring Group shi ne wanda ake sa rai zai tsaya takarar Birnin Kano a NNPP.

An tsaida masu takara

Tsohon Kwamishinan kudi na jihar Kano, Shehu na Allah ya samu tikitin 'dan majalisar wakilan tarayya duk da sai a jiya aka ji labarin shigansa jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

Legit.ng Hausa ta fahimci sauran matasan da ba za su samu tikitin NNPP ba sun hada da Rabiu Juda, Mahbub Ibrahim, Aliyu Kankarofi, da irinsu Musaddiq Tofa.

Sharada ya tafi, ya dawo

Mun nemi jin ta bakin Sharada a yau da safe, amma 'dan siyasar ya kashe duka wayoyinsa. Sai daga baya mu ka ji cewa ya bada sanarwar dawowansa PDP dazu.

Yusuf Sharada ya ce ya yi kuskuren sauya-sheka, amma ya nemi afuwar abokan tafiyarsa. Har ila yau, ya yi watsi da tayin da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi masa.

Ni Yusuf Sharada Ina sanar da mutane cewa gaskiya ne jiya mun gana da gwamna Ganduje, bayan komawar Jagora Rabiu Kwankwaso Abuja. Ajizanci na Dan Adam ya jani ga yanke hukunci wanda bai yiwa 'yan uwa da masoya dadi ba. Ina bawa dukkan wanda wannan abu da nayi ya batawa rai hakuri.
Matsayar dana dauka ta samu rashin goyon bayan iyaye, 'yan uwa da abokan arziki daga sassa daban daban na kasar nan.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Shekarau ya karbi katinsa na zama cikakken dan jam’iyyar NNPP

Gwamna Ganduje bai bani koda naira daya ba, kuma offer daya bani nayin aiki dashi na hakura da ita.
Zan cigaba da yin abinda aka sanni akansa, in shaa Allah.
Kwankwasiyya Amana!

- Yusuf Sharada

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng