2023: Maza sun gaza, cikin wata 6 mata da matasa za mu gyara Najeriya, 'Yar takarar APC
- 'Yar takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar APC, Uju Ken Ohanenye ta bayyana damuwarta a kan yadda maza suka gaza samar da ingantaccen mulki a Najeriya
- Ta sanar da cewa ba ta so ta yi magana ba, amma yadda ta ga kasar na tafiya ne yasa ta zaburo ta kawo gyara tunda maza sun gaza yin hakan
- 'Yar takarar ta sanar da cewa za ta tabbatar da cewa ta bai wa mata da matasa ragamar mulkin kasar ta yadda cikin wata 6 kacal za a ga sauyi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Matar dake takarar shugaban kasa karkashin jam'iyya mai mulki (APC), Uju Ken Ohanenye ta nuna damuwa a kan abun da ta siffanta da gazawar maza wajen samar da ingantaccen mulki a Najeriya.
Yayin tattaunawa a talabijin na Arise a Legas, ranar Laraba, ta bayyana yadda za ta yi mulki yadda ya dace da halayyar uwa ga 'ya'yanta ga gwamnati don bambamta da saura.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Na yi shiru ne tsawon wannan lokacin. Ban so shiga ciki ba, amma yadda abubuwa suke tafiya yasa ba zan iya cigaba da shiru ba, saboda ina shiga cikin damuwa yadda ba na ganin abubuwa yadda ya kamata su kasance. Hakan yasa na fahimci cewa 'yan Najeriya na bukatar a fuskancesu.
"Na yanke shawarar shiga ciki. Ina so in bada gudunmawa. Ina so in bambamta da sauran, mazan sun gaza. Saboda haka na fito domin 'yan Najeriya na bukatar Uwa. Suna bukatar 'diya. Maza sun dade suna mulki na tsawon lokaci.
"Ya kamata mu taimaki kawunanmu. Ya kamata mu hada kai don gyara kasarmu sannan a matsayina na uwa, zan iya tsara yadda kowa zai zo wajen gyara kasar. Zan jawo kowa a bada gudunmawa wajen kawo cigaba ga yankin shi," ta ce.
Ohanenye ta ce, idan aka zabe ta shugabar kasa, za ta maida hankali wajen tallafawa matasa da sana'oin da zasu samu damar magance manyan matsaloli.
Mulkinta zai ba matasa damar yin nasara
"Yawanmu karin tattalin arzirki ne. Akwai abubuwa da dama da za mu iya taimakawa matasanmu wajen samu duk da ya dogara da yadda za su iya aiki. Matasanmu basa bukatar fita kasar waje don su bautar da kawunansu."
Game da takamaimiyar hanyar da zata samar da aikin yi, ta ce za ta maida Najeriya ta rage dogaro da man fetur, sannan ta maida hankali a bangaren noma tare da kayan noma na zamani don bude kasuwar wajen samar da arziki.
Ohanenye ta bukaci mata da kada su kashe ma ta kwarin guiwa da irin mulkin siyasa a kasar, a cewar ta dole ne matan Najeriya su yi dubi da 'ya'yansu da harkar tsaro ta hanyar shiga siyasa.
Asali: Legit.ng