Na hannun daman Buhari zai yi takarar Gwamna da mutane 8 bayan rasa kujera a APC
- Hon. Farouk Adamu Aliyu ya fito neman takarar gwamna a jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar APC
- Tsohon ‘dan majalisar ya yi kira ga Gwamnan Jigawa ya bari ayi adalci wajen fito da ‘dan takara
- Farouk Aliyu ya taba rike shugaban marasa rinjaye a lokacin da yake majalisar wakilan tarayya
Jigawa - Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Farouk Adamu Aliyu ya bada sanarwar neman takarar gwamna a jihar Jigawa a zaben shekarar badi.
Premium Times ta ce Hon. Farouk Adamu Aliyu ya shaidawa Duniya wannan ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a garin Dutse, a jihar Jigawa.
Farouk Adamu Aliyu ya yi kira ga Gwamna mai-ci, Mai girma Muhammed Badaru Abubakar ya guji yin katsalandan wajen zaben fitar da gwanin APC.
‘Dan siyasar ya roki Muhammed Badaru Abubakar ya bari a tsaida duk wanda jam’iyya ta ke so.
“Mu tara da ke neman gwamna a karkashin APC mun san kanmu, mu na girmama junanmu, mu na magana da juna.”
“Ba takarar fada mu ke yi ba, yakin neman darewa kan kujera mai daraja ne domin mu yiwa mutanenmu hidima.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ko da yake ba tantamar adalci da gaskiyar Gwamna Badaru na ke yi ba, sau uku yana cewa bai da ‘dan takara.”
“Badaru ya yi alkawarin zai taimaka wajen ganin jam’iyyar APC ba ta sha kashi a Jigawa a zabe mai zuwa ba.”
- Farouk Adamu Aliyu
Ba zan janye ba - Farouk Aliyu
Rahoton Daily Post ya nuna cewa Aliyu bai da niyyar hakura da takarar da ya sa gaba. Idan ya karbi mulki, ya sha alwashin hukunta masu saba doka.
Idan tsohon ‘dan majalisar tarayyan na Birnin Kudu/Buji ya yi nasarar zama gwamna, ya ce zai bada karfi a harkar noma, wanda da shi aka dogara a jihar.
Aliyu zai taimakawa manoma da takin zamani da iri cikin rahusa saboda talaucin da ake fama da shi.
‘Dan siyasar zai kula da kiwon lafiya, ganin adadin yara da mata da ke mutuwa a Jigawa. Jaridar ta ce Hon. Aliyu ya yi alkawari zai ba ilmi muhimmanci.
Takarar shugaban kasa
Felix Morka ya shaidawa ‘yan jarida cewa mutane 28 suka cire N100m domin sayen fam din neman shiga zaben shugaban Najeriya a jam’iyyarsu ta APC.
Kakakin na jam’iyyar APC mai mulki ya ce mutane uku ne ba su dawo da fam din su ba. Wannan yana nufin APC ta tashi da akalla Naira biliyan 2.8 tun a nan.
Asali: Legit.ng