Karin bayani: Shekarau ya karbi katinsa na zama cikakken dan jam’iyyar NNPP
- Ta tabbata tsohon gwmanan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya sauya sheka zuwa NNPP mai tasowa ta su Kwankwaso
- Sanatan mai ci ya karbi katin zama cikakken dan jam'iyya a yau Laraba a gidansa da ke Mundubawa a jihar Kano
- Ilahirin masoya da magoya baya ne suka halarci taron, wanda majiyoyi da dama suka rahoto yadda ya faru
Jihar Kano - Sanata Ibrahim Shekarau na jihar Kano ya karbi katin shaidan zama dan jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) mai tasowa, Daily Trust ta rahoto.
Sanatan wanda aka zabe shi a zauren majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar APC ya fice daga jam’iyyar ne biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin tsaginsa da na Ganduje.
Dubun dubatar magoya bayansa ne suka shelanta sauke shekarsu a gidansa da ke Mundubawa.
Tsohon gwamnan na jihar Kano kuma jigon NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya halarci taron sauya shekar Shekarau a hukumance ya mika masa katin zama dan jam’iyyar NNPP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wadanda suka halarci taron sun hada da masu ruwa da tsaki a siyasar Kano da magoya bayansu a sansanin Kwankwasiyya da shugabannin majalisar Shura na tsagin Malam Shekarau da sauran masu fada aji.
Wasu hotuna da shafin Twitter na NNPP Worldwide Platform ya yada ya nuna lokacin da masoya Kwankwaso da Shekarau suka taru a kofar gidan Sanatan a daidai lokacin da Kwankwaso ya iso domin mika takardar shaidan shiga jam'iyyar.
Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar
A wani labarin na daban, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman kujeran shugaba a 2023 karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya jaddada cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa a 2019.
Atiku yace kawai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amfani da karfin mulki wajen kwace nasarar daga hannunsa.
Ya kara da cewa sam ba zasu taba yarda a sake musu irin wannan a zaben 2023 idan jam'iyyar PDP ta bashi tikiti.
Asali: Legit.ng