Sanusi II: Kamar yadda APC ta yi ciniki bana, Allah yasa Nasarawa ta samu masu zuba jari

Sanusi II: Kamar yadda APC ta yi ciniki bana, Allah yasa Nasarawa ta samu masu zuba jari

  • Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi addu'an samun masu zuba jari a jihar Nasarawa
  • A addu'an nasa, Sanusi II ya roki Allah da ya kawo masu zuba jari a jihar kamar yadda ya kawowa APC ciniki daga yan takarar shugaban kasa a bana
  • Wannan addu'a na tsohon sarkin ya baiwa mahalarta taron dariya ciki harda tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yiwa jihar Nasarawa addu’an samun masu zuwa hannun jari da za su zo su zuba jari a cikinta.

Sanusi ya yi jawabi a taron zuba jari na Nasarawa na 2022 (#NIS2022) wanda aka gudanar kwanan nan, jaridar The Cable ta rahoto.

Tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama, ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen taron.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

Sanusi II: Kamar yadda APC ta yi ciniki bana, Allah yasa Nasarawa ta samu masu zuba jari
Sanusi II: Kamar yadda APC ta yi ciniki bana, Allah yasa Nasarawa ta samu masu zuba jari Hoto: unsdgadvocates.org
Asali: UGC

Da yake jawabinsa cike da raha, Sanusi II ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ga mai girma gwamnan jihar Nasarawa, ina addu’an Allah ya kawo tarin masu zuba hannun jari jiharka kamar yadda ya kawo yan takarar kujerar shugaban kasa ga APC."

Da yin wannan addu’a nasa sai mahalarta taron suka kaure da dariya harda Mahama.

Ga bidiyon addu'an nasa:

Ba tare da la’akari da tsawwala kudin fom din takarar shugaban kasa na APC da farashinsa ya kai naira miliyan 100 ba, fiye da yan takara 20 ne suka ayyana aniyarsu ta neman kujera ta daya a kasar a karkashin inuwar jam’iyyar mai mulki.

Wasu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas; Rotimi Amaechi, ministan sufuri; Dave Umahi, gwamnan jihar Ebonyi.

Sauran sune Rochas Okorocha, tsohon gwamnan Imo; Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi; Emeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi; Ogbonnaya Onu, ministan kimiyya da fasaha; Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti; Godswill Akpabio, Ministan Neja Delta, da sauransu.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Ba zan sarara ba a siyasa har sai na mulki Najeriya

Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya

A wani labarin, mun ji cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na ci gaba da samun garumin goyon baya a takararsa na son mallakar tikitin shugaban kasa na jam’iyya mai mulki.

PM News ta rahoto cewa wani bincike daga mabiya jam’iyyar a Kano, Kaduna, Katsina, Neja, Adamawa da wasu yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma ya nuna cewa babu wani dan takara da wakilai ke ganin mutuncinsa kuma suka yarda da shi kamar Tinubu.

Hakazalika shine ya samu tarba mai kyau sannan aka bayanna shi a matsayin jajirtaccen shugaba kuma dan jam’iyya na gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng